✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Cakwakiyar musayar ’yan wasa 5 da ke gaban Chelsea

Arsenal na son daukar Sterling daga Chelsea.

A halin yanzu cakwakiyar musayar ’yan kwallo ta yi wa Chelsea lullubi gabanin karkare kakar wasanni ta bana.

Chelsea na duba yadda za ta dawo da Tammy Abraham kungiyar daga Roma, wanda zai fi dan wasan Napoli, Victor Osimhen Arha. (Football Insider)

Shugaban Inter Milan, Giuseppe Marotta ya ce Romelu Lukaku zai koma Chelsea a karshen kakar bana, bayan kammala wasannin aro a kungiyar. (Sky Sports Italia)

Arsenal za ta so daukar dan kwallon Chelsea, Raheem Sterling idan har za a sayar mata da shi a karshen kakar nan. (90 Min)

Chelsea na fuskantar kalubale, bayan da Mason Mount da kuma Ruben Loftus-Cheek, suka shiga kakar karshe a kwantiraginsu da Stamford Bridge. (Mirror)

%d bloggers like this: