✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Burinmu shi ne bunkasa adabin Hausa a duniya – Abu Hidaya

Malam Rabiu Muhamamd (Abu Hidaya) shi ne Shugaban rikon kwarya na kungiyar Tsangayar Adabin Hausa, a hirarsu da Aminiya ya bayyna dalilan kafa wannan tsangaya…

Malam Rabiu Muhamamd (Abu Hidaya) shi ne Shugaban rikon kwarya na kungiyar Tsangayar Adabin Hausa, a hirarsu da Aminiya ya bayyna dalilan kafa wannan tsangaya da kuma irin ayyukan da take yi gudanarwa wajen ciyar da adabin Hausa gaba.
Aminiya: Wadane manufofin suka sa kuka kafa wannan tsangaya?
Abu Hidaya: Mun kafa wannan tsangaya ta adabin Hausa a shekarar 2011, inda muka yi taronmu na farko a tsohuwr Jami’ar Bayero inda muka samu gamayyar ra’ayi na masu kishin adabin Hausa, wadanda suka hada da mawaka da marubuta. Manufofin kafa wannan tsangaya sun hada da farfado da bunkasa adabin Hausa da tattara ayyukan adabin Hausa na da, da na yanzu, da kuma samar da sababbin bincike a nazarin adabin Hausa. Kwarmata adabin Hausa a kafafen watsa labarai  da kuma shirya tarurrukan ilimi domin kara wa juna sani da kuma fitowa a fili yadda adabin Hausa zai inganta ilimi da zamantakewa da tattalin arzikin al’umma. Bai wa hukumomi  da kungiyoyi shawarwarin da za su bunkasa adabin Hausa. kulla alaka da masana adabin Hausa a ko’ina a duniya da kuma hukumomi masu tallafa wa adabi.
Aminiya: Zuwa yanzu wadanne irin ayyuka wannan tsangaya ta aiwatar?
Abu Hidaya: Babu shakka zuwa dan wannan lokaci mun samu nasarar aiwatar da ayyuka masu yawa. A kawanan baya mun gudanar da taron kara wa juna sani inda muka shirya wa mata dari biyu bita akan dabarun tarbiyyar yara a Musulunci da al’ada da kuma muhimmancin neman ilimi. Haka kuma mun yi tatattaki har zuwa kasar Nijar don bunkasa adabin Hausa, inda muka gudanar da wasannin kwaikwayo da wakoki. Ina ganin wannan ba karamar nasara ba ce a gare mu. A yanzu haka muna da shirye-shiryen gudanar da wani babban taro, inda za mu hada kungiyoyin marubuta da mawaka domin farfadowa tare da bunkasa adabin Hausa.  Haka kuma a yanzu mun fara yin mujalla tamu ta kanmu, wacce muke fito da rayuwar wasu mutane da suka shafi masarautu, musamman wadanda rayuwarsu ta ta’allaka wajen taimaka wa jama’a da son ciyar da al’umma gaba. Mun yi wa mujallar shiri sosai na samun bayanai da kuma amfani da kudi. Yawanci mutumin da za mu sa a mujallar shi ke daukar nauyin aikin da kansa
Aminiya: Wane irin kalubale kuke fuskanta tun bayan kafa wannan tsangaya?
Abu Hidaya: A duk lokacin da mutum ya so yin abin alheri sai ya fuskanci matsala. Akwai matsaloli da muke fuskanta sai dai zuwa yanzu muna ta kokarin magance su. Akwai rashin halartar taro akan lokaci daga membobi da shugabannin rikon wannan tsangaya, duk da cewa ba na shakkun hadin kai a tsakaninmu.
Aminiya: Ko wannan tsangaya ta kulla alaka da gwamnati ko wasu kungiyoyin?
Abu Hidaya: A gwamnatance zan iya cewa muna da alaka da Hukumar Tace Fina-finai da kuma Hukumar Adana kayayyakin tarihi da al’adu ta Jihar Kano (History & culture bureau).  Haka kuma muna da burin kulla alaka da hukumomi da kungiyoyi masu zaman kansu irin su UNESCO da sauransu. Haka kuma idan kika dauki jami’o’iw, muna da alaka da bangaren nazarin harshen Hausa na Jami’ar Jihar Kaduna da kuma Jami’ar Bayero ta Kano. Idan kika dauki Farfesa Ibrahim Malumfashi da Farfesa Abdulkadir dangambo da Farfesa dandatti Abdulkadir  da Farfesa Sa’idu Gusau duk wadannan mutane ne da suke tare da mu. .A yanzu haka kuma mun kulla kawance mai karfi da gidan Rediyon Sahara a Agadez ta kasar Nijar, a yanzu haka ma sun ba mu wani fili da za mu rika gabatar da wani shiri namu, sai dai yanayin nisa ya sa har zuwa yanzu ba mu fara komai ba, amma da zarar mun kammala aikace-aikacenmu za mu duba yiwuwar yadda al’amura za su kasance.
Aminiya: Wadanne hanyoyi  wannan tsangaya ke bi don samun kudin shiga?
Abu Hidaya:  zuwa yanzu dai ba mu da wata hanya da muke samun kudi, duk abin da muke yi da aljihunmu muke yi. A duk wata akwai abin da muke fitarwa daga aljihunmu. Sannan akwai kudin rajista da muke karba daga membobinmu.  Sai kuma mujalla da muke kokarin samarwa wacce ita ma hanya ce da za mu rika samun kudin shiga daga gare ta.
Aminiya: Shin wannan tsangaya ta tsaya ne iyakacin Kano ko kuwa har kasa baki daya?
M. Rabiu: Kasancewar mu da muka kafa wannan tsangaya mazauna Jihar Kano ne zan iya cewa ta fi karfi a Kanon, duk da cewa muna da reshe a Jihar Katsina da Kaduna da Jigawa. A kasar waje kuma muna da rassa a Agadas da Zindar ta kasar Nijar.    
Aminiya: Mene ne sakonka ga masu kishin adabin Hausa?
Abu Hidaya: Sakona ga al’umma shi ne a duk lokacin da mutum ya bayyana zai yi wani abu, to ya kamata a dubi abin nan a gano cewa mai amfani ne ga jama’a ko kuma kishiyarsa.Wannan tsangaya ta zo da abubuwan  alkhairi masu yawa, wadanda za su bunkasa ilimin al’umma tare da tattalin arzikinsu. Sannan mukan bi makarantu mu shirya musu muhawara a tsakaninsu don farfado da hazakarsu. Haka kuma ta fuskar tattatlin arziki mukan shiga kafafen watsa labarai mu yi magana akan wani abu da ya shafi tattalin arzikin kasa. Idan mutane sun ba mu hadin kai insha Allah nan gaba kadan duk wani abu da ake ganin mutane suna samun ci gaba ta hanyar yarensu, to mu ma za mu yi don ci gaban harshen Hausa. Harkar yanar gizon nan da kimiyya duk muna son samar da na Hausa tsantsa, ma’ana yadda za a Hausantar da komai. Muna da burin kafa tarihi na kawo ci gaban da ba a taba samu ba wajen ciyar da adabin Hausa gaba a duniya.