Aminiya ta zanta da wani matashin yaro mai kwazo, wanda Allah Ya ba hikima da basira na kirkire-kirkire da zanen mota.
Anas Abdullahi Makera dan asalin Dutsenma a Jihar Katsina, ya bayyana wa Aminiya cewa wani shugaban dalibai a makarantarsu mai suna Anas Bilbis ne ya ba shi shawara da su zo su nemi Jelani Aliyu domin su nuna masa irin baiwar da Allah Ya ba Anas Makera tunda ya taba ganin zanen da ya yi kuma ya yaba tun yana kasar waje.
“Gaskiya tun ina yaro nake sha’awar zane, kuma zan iya cewa kawai Allah ne Ya ba ni basira da hikimar da nake amfani da ita. Kusan mutane sun sanni, ko ana zaune ne kawai za ka ga ina ta zane. Da mahaifina ya lura cewa ina son zane, sai ya ce zai kai ni makarantar da zan koyi zane. Bayan na kammala makarantar Sakandiri, sai na nemi gurbin karatu a kwalejin Kimiyya da Fasaha na Hassan Usman da ke Katsina, inda na nemi gurbin karatu a fannin zanen gideje (Architecture) saboda babu fannin da na fi sha’awa wato zanen mota.
“Yanzu haka ina karatu ne a kwalejin, amma saboda yadda na yi fice har a wajen malamai, sai mutane suke bani shawara da na zo na nemi ganin Jelani Aliyu tun da shi ne shugaban Hukumar kirkire-kirkiren motoci, kuma shi ma da haka ya fara, shi yasa nake so na ganshi ko zai taimaka min, nima na samu daman a nuna wa duniya irin basirar da Allah Ya bani,” inji Anas.
Da ya juya kan yadda ya tsinci kanshi cikin harkar zane-zane, Anas cewa ya yi “kawai sha’awa ce. Yawancin lokaci nakan zauna ne in zana mota kawai domin na ji dadi. Kuma ina jin dadi idan na ji mutane suna cewa ina kokari sasai. Yadda mutane ke jin dadin da yabawa idan na yi zanen ne ke kara min karfin gwiwar har na ji ina so in ci gaba.
“Kuma na karanta tarihin Aliyu Jelani, sai na lura cewa muna kama ta hanyoyi da dama. Da farko dai yadda ya fara, nima haka na fara. Kuma kusan duk yadda ya yi jawabin yadda yake zane da tsara mota, nima haka nake,” inji Anas.
Da wakilin Aminiya ya tambayeshi ko ya taba tuntubar Jelani Aliyu din a lokacin baya, sai Anas ya ce “Tun yana kasar waje nake tuntubarsa, na tura mai sako da gutunan motocin da na zana ta Imel kuma ya maido min da jawabi kuma ya yaba sosai. Shi yasa yanzu nake so na ganshi tunda ya taba ganin aiki na, kuma ya yaba,” inji Anas Makera.