✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Burina in zama fitaccen mawakin Hausa – Badamasi Alhassan

Aminiya ta zanta da wani mawaki mai suna Badamasi Alhassan, wanda ana iya cewa ya shigo harkar waka da sa’a domin tun shigowarsa tauraronsa ke…

Aminiya ta zanta da wani mawaki mai suna Badamasi Alhassan, wanda ana iya cewa ya shigo harkar waka da sa’a domin tun shigowarsa tauraronsa ke haskawa, wanda shi kansa ya ce abin na ba shi mamaki matuka. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

 

Aminiya: Za mu fara da gabatar da kanka ga masu karatu?

Sunana Badamasi Alhassan. An haifeni a garin Rigo da ke karamar hukumar kafur, a Jihar Katsina. Na yi karatu na Muhammadiya da na boko daidai gwargwado a kafur. Sannan daga baya na yi kaura na dawo garin Abuja inda nake zaune yanzu haka. Kuma yanzu ina da kimanin shekara 25 a duniya.

Aminiya: Me ya ja hankalinka ka shiga harkar wake-wake?

Eh! To gaskiya abin da yasa na shiga harkar waka shi ne na kasance mai matukar shaukin wakokin Hausa tun ina karami, sannan kuma na kasance tun ina karami na kan rera waka ba tare da na rubuta ba. Har wasu su kan yi mamakin yadda nake rera waka a wancan lokacin. sannan kuma da yake na ga hanya ce da zan isar da sako cikin sauki, domin mutane da yawa suna sauraron wakoki. To da nag a cewa mutane na son wakoki, shi ne ni kuma na shiso harkar domin in kawo bambanci a lamarin ta hanyar isar da sako.

Aminiya: Wakokinka nawa yanzu kuma wane irin wakoki kake yi?

Gaskiya na rubuta wakoki da yawa. Amma wadanda ake ji yanzu sun kai akalla 10. Saboda a hankali ake farawa, kuma abin na bukatar tunani domin a ba mutane abin da suke so, kuma su nishadantu. Sannan kuma abin na bukatar kudi. Kuma ya zuwa yanzu na kai kimanin shekara 3 a cikin wannan harkar. Sannan kuma Allah Ya saukakemin waka, domin yanzu haka ina yin wakokin aure, biki, suna da sauransu. Sannan kuma na gaba kadan da yardarm Allah za a fara amfani da wakokina a cikin finafinan Hausa.

Aminiya: Ko kana da wani mai gida a wannan harkar ta waka?

kwarai kuwa ina da mai gida. Mai gidana a wannan harkar shi ne Sagir Usher. Shi ne ya sa ni a hanyar wannan hakar, shi ya fara nuna min yadda zan yi waka da kuma yadda zan rubuta wakar. Sannan kuma har yanzu na kan je wajensa mu yi shawara idan ina rubuta waka, sannan kuma kullum baya gajiyawa wajen ba ni shawara a kan yadda zan yi.

Aminiya: Menene burinka a wannan harkar?

Gaskiya burina shi ne in zama wani fitaccen mawaki da za a rika jin duriyata a Najeriya, da ma duniya baki daya. Wannan ne burin kowane mawaki a ko ina yake a duniya. Waka wata hanya ce ta shahara, don haka burina na shahara, sannan kuma in taimakawa na kasa da ni domin suma su dago.

Aminiya: Ko kana kira zuwa ga sauran mawaka ’yan uwanka?

Ina kira ga dukan mawaka na sama da ni, da na kasa da ni da wadanda muke sa’anni da cewa mu rike sana’ar da mutunci. Mu rika mutunta kanmu, kuma mu tsaftace sana’ar. A kullum mutane suna mana wani irin kallo, saboda a tunaninsu mu mutanen banza, to ya kamata mu nuna musu cewa lamarin ba haka ba ne. Mu nuna musu cewa mu burinmu shi ne mu nishadantar da su, kuma mu natsar da su. sanana kuma mu rage hasada. Mu hada kai mu taimaki sana’ar, sannan kuma mu rika taimakon juna.

Aminiya: Ko kana da sako zuwa ga masoya?

Ina kira ga masoya da cewa idan su ji kuskure, su rika kira suna mana gyara, domin dan Adam ajizi ne. kuma su rika mana addu’a da fatan alheri. A kullum Hausawa na cewa fata na gari lamiri. Don haka a rika taimaka mana da addu’a domin mu samu dama da jin dadin nishadantar da ku. Na gode.