✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Burina in tarbiyyantar da al’umma – Dokta Amina Haruna Abdul

Dokta Amina Haruna Abdul,Wakiliyar Tula, babbar  malama ce a Kwalejin Ilimi (Kere-Kere) ta Tarayya (FCE -T) da ke Gombe. Har ila yau mawallafiya ce da…

Dokta Amina Haruna Abdul,Wakiliyar Tula, babbar  malama ce a Kwalejin Ilimi (Kere-Kere) ta Tarayya (FCE -T) da ke Gombe. Har ila yau mawallafiya ce da ta rubuta litattafai da kasidu da dama don amfanin daliban kwalejojin ilimi da na jami’oi. Yanzu haka ta shafe kimanin shekara 40 tana koyarwa a matakai daban-daban.  A zantawarta da wakilinmu, ta yi bayanin tarihin rayuwarta da kalubalen da ta fuskanta da kuma nasarorin da ta samu:

Tarihin rayuwata:

Sunana Dokta Amina Haruna Abdul.  Ni ’yar kabilar Tula ce daga Karamar Hukumar Kaltungo a Jihar Gombe.    A Tula aka haife ni a ranar 10 ga watan Fabrairun1960. A can na yi kuruciya har na girma iyayena suka sa ni a makarantar firamare ta Baule/ Gadau a1966 zuwa 1971, bayan na kammala sai na tafi   Kwalejin Horar da Malamai Mata (WTC) da ke Azare, inda na samu  takardar shaidar karatu mai daraja ta biyu (Grade II) a 1972 zuwa 1976. Kuma na shiga Kwalejin Ilimi (COE) da ke Azare, a Jihar Bauchi inda na samu takardar shaidar ilimi ta kasa (NCE) a  1979 zuwa 1982. Sai na tafi hidimar kasa a 1982 zuwa 1983 a garin Bauchi domin a wancan lokacin idan mutum ya gama karatun NCE zai yi hidimar kasa kamar yadda masu digiri suke yi a yanzu. Bayan nan sai na tafi Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya a 1984 na gama a  1986. Na karanta ilimin tattalin gida (Home Economics) sannan na yi digiri na biyu a Jami’ar Jos daga 1992 zuwa 1998 inda na karanta yadda ake jagoranci da koya wa yara tarbiyya.

Sai kuma a shekara ta 2004 na karanta ilimin kwamfuta a Kwalejin Ilimi ta Tarayya (Kere-Kere-  FCE (T) da ke nan Gombe, wato inda nake koyarwa. Sannan na yi digirin digirgir (digiri na uku) a bangaren tattalin a Jami’ar Ahmadu Bello da ke  Zariya.

Aiki:

Na fara aiki ne a matsayin malamar makaranta a firamare ta Yayu da ke garin Katagum a Jihar Bauchi daga 1976 zuwa 1977 daga nan na koma firamare ta St, Judes da ke Legas a 1977 zuwa 1979, sai na koma  Kwalejin Horar da Malamai Mata ta garin Azare a Jihar Bauchi a tsakanin 1982 zuwa 1983 a lokacin da nake yi wa kasa hidima. Bayan nan na koma WTC Azare daga 1983 zuwa1986, ina wannan kwalejin ta ’yan mata sai na koma koyarwa a Kwalejin Ilimi ta garin Azare, (COE) a 1986 zuwa 1998.  Daga nan ne na koma Kwalejin Ilimi ta Tarayya wato FCE (T) Gombe daga 1998 zuwa yau.

Nasarori:

A gaskiya kasancewata malamar makaranta na samu nasarar koyar da mata yadda za su yi zaman aure da mazansu da kuma yanayin zamantakewa na rayuwa saboda wadansu matan mazansu ba sa barinsu su shiga makaranta.   Na shiga kwamitoci daban-daban na harkar mata don ganin na kare hakkokinsu wannan ma nasara ce.

Kalubale:

Batun gaskiya akwai kalubale masu yawa domin hada aikin ’ya mace da namiji a waje daya akwai kalubale saboda ba kowace mace ce za ta iya daurewa ta yi aiki a tsakanin maza ba, ga kuma hada ayyukan gida da na ofis ga tarbiyar yara.  Idan mace ba ta yi sa’a ba sai ka ga aure ya mutu. Sannan  idan mace tana aiki amma ba ta yi sa’ar mijin da zai rika ba ta shawarwari da goyon baya ba, za ta fuskanci kalubale da yawa.  Har yanzu kuma akwai irin mazan nan da suke ganin ba za su iya yin aiki a karkashin mace ba, idan Allah Ya daukaka ta ya ba ta shugabanci saboda suna ganin ke mace ce suna da kamarki a gida ka ga dole matsala za ta taso.

Yawan iyali:

Alhamdulillahi godiya ga Allah ban samu haihuwa da wuri ba, amma duk da haka Allah Ya albarkace ni da ’ya’ya biyu, namiji da mace. Namijin ya gama jami’a, ita kuma macen tana shekarar karshe a jami’a.

Kungiyoyi:

Na taba zama mamba da kuma shugabancin kungiyoyi masu yawa amma kadan daga ciki su ne Kwamitin Ilimin Kwamfuta na Kwalejin FCE (T), Gombe, sai Sakatariyar Kungiyar Malaman Kwalejojin Ilimi (COEASU) da Shugabar Mata ta Kwalejin Ilimi (Women in Collage of Education-WICE) ta Gombe da kuma  Shugabar Sashin Koyar da Sana’o’i  ta Kwalejin Ilimi ta Gombe da sauransu.

Kasashen da na taba zuwa:

Ba ni da shawa’ar zuwa wata kasa a duniya saboda ba sa gabana amma dai na je Saudiyya kuma ina da sha’awar sake komawa nan gaba.

Abin da na fi so a tuna ni da shi.

A gaskiya abin da na fi son a rika tunawa da ni shi ne duk in da

 

dalibina ya gan ni ya ba ni shaida tagari kasancewa ta dadaddiyar malamar makaranta kuma zan ji dadi idan na ga dalibin da na koyar ya zama wani abu a rayuwa. Yanzu haka cikin dalibaina akwai wadanda suka kai wani matsayi a kasar nan, kamar Kwamandar Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (Cibil Defence) ta Jihar Gombe, daliba ta ce a Kwalejin COE da ke Azare. Wannan ma abin alfahari ne gare ni.

Burina a rayuwa:

Idan na yi ritaya na bar aiki ba ni da burin yin siyasa kamar yadda wadansu suke ba ni shawarar shiga siyasar. Sai dai ina da burin in bude makaranta ina karantar da yaran unguwa da nawa, koda na bar aiki saboda aikin malanta aiki ne na sadaukar da kai.

Lambobin yabon da na samu:

Na samu lambar yabo ta dalibar da ta fi yin fice a lokacin da nake Kwalejin Ilimi ta Azare a 1986, sannan  Kungiyar Dalibai ta Kaltungo da Shongom reshen Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke garin Bauchi ta karrama ni da lambar yabo ta wacce take taimaka wa harkar ilimi a  Masarautar Kaltungo. Na kuma samu lambar yabo kan yadda na gudanar da shugabanci a lokacin da nake shugaba ta shiyyar Arewa maso Gabas ta Kungiyar Women in College of Education – WICE)  ta Yola.

Shawararta ga mata:

A matsayina ta uwa ina bai wa ’yan uwana iyaye mata shawarar su daure su rika sanya ’ya’yansu mata a makarantar boko inda za su samu ilimin zamani bayan na addini da suke yi da zai kai su ga dogaro da kansu ko da bayan sun yi aure ne ta hanyar rage wa mazansu dawainiyar gida. Ba ilimin addini ne kadai abin nema ga ’ya’ya mata ba har da na boko, saboda a gaskiya jahilci ne a bar mata kara-zube ba ilimi. Domin idan aka ce yau mace ba ta da ilimi, ko tarbiyyar ’ya’yanta ba ta san ta inda za ta fara ba. Sannan yana da kyau iyaye su  gane cewa hana ’ya mace karatu sai tallace-tallace shi yakan  jefa rayuwarsu cikin bala’i domin ta hanyar talla ce mafi yawansu suke jawo wa iyayensu abin takaici.  Da fatan Allah Ya sa mu dace.