Aminiya ta zanta da matashiyar jaruma a masana’antar Kannywood, Amina Rani wadda tsohuwar matar Adam A. Zango ce, inda ta bayyana yadda fim da ita da Zango zai kasance da burinta na shiga fim da sauransu.
Za mu fara da tarihinki a takaice
Sunana Amina Uba Hassan, amma an fi sanina da Amina Rani. An haife ni a Kaduna. Na yi firamare a makarantar NTI, na yi sakandare a Queen Amina. Sai kuma Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kaduna (Kaduna Polytechnic), inda na yi Diploma.
Yanzu haka ina kasuwanci, sannan ina da gidauniyar taimakon al’umma da nake gudanarwa, sannan nan ba da jimawa ba zan ci gaba da karatu.
Yaya aka yi kika tsinci kanki a harkar fim?
Na taso ina kallon fina-finai. Sai dai na fi son kallon fina-finan Indiya da Amurka, ban cika kalon fina-finan Hausa ba, sai dai idan na zo na ga ana kallo, in zauna mu kalla. Sannan kuma tun da can, ina son rawa.
Akai wani mutumina, Bello Sharukhan, yana da kungiyar rawa, sai na shiga.
To watarana na zo Abuja, sai a kusa da mu na ga ana daukar wani fim na Kudu, sai abin ya ba ni sha’awa.
Na je muka gaisa da jarumin fim din. Daga nan ne sai abokaina suka fara ba ni shawarar in fara fim mana, tunda na iya Turancin Ingilishi da Hausa, suna cewa zan iya fitowa a fina-finan Arewa da na Kudu.
Daga wannan shawarwarin da suka ba ni, shi ke nan fa abin ya fara shiga min rai. Ka ji yadda na fara.
Ke nan za ki rika fitowa a fina-finan Kudu?
Ina sha’awar fina-finan Kudu, sai dai akwai wasu abubuwa da ba zan iya yi ba.
Duk da cewa mun rabu da mijina, amma ina da da dole in kare masa mutuncinsa.
Sannan yanayin al’adunmu da addini, ba zai yarda da wasu tsare-tsaren fina-finan Kudu ba.
Wannan ne ya sa ban wani damu da shiga ba, na fi mayar da hankali a Kannywood.
Sannan tsohon mijina, Adam A. Zango na nemi shawararsa, ya ce min Nollywood sun fi Kannywood hadin kai, amma da na fada masa uzurina, sai ya amince.
Sannan a matsayin sabuwar jaruma, ba zai yiwu in cika zabar fina-finan da zan fito ba, domin idan na fara da hakan, masu shirya fina-finai ba za su damu da nema na ba.
Wannan ya sa na tsaya a Kannywod, amma kuma ba mu san abin da Allah Zai yi ba nan gaba.
Ba ki dade ba da shigowa Kannywood, amma ana ta maganarki, za a iya cewa saboda kasancewarki tsohuwar matar Zango ce?
Duk lokacin da na fita, sai ka ji ana ga Maman Haidar.
Lokacin da muka yi aure babu kafofin sadarwa sosai. Don haka babu hotunanmu da yawa.
Da an ji an ce tsohuwar matar Zango, kowa zai so ya gan ni, don haka na san dole akwai wannan jan hankalin, amma na fi son a sanni da sunana.
Na fi son in zama fitacciyar jaruma Amina Rani. Amma na san ba zai yiwu in raba sunana da na Adamu ba; mun yi soyayya sosai, muka yi biki mai girma, sannan muna da da tare.
Amma duk da haka, na san zan iya yin sunana na kaina.
Ki ba mu labarin fim dinki Jaruma 2?
Fim din Jaruma 2, ci gaban Jaruma 1 wanda furodusa Ibrahim Sharukhan ya shirya.
A na farkon, jaruma Maryam Yahaya ce ta ja fim din, inda ta shigo fim ba tare da amincewar iyayenta ba, ta samu daukaka, sannan daga baya ta fara raina manyanta.
Sai na shigo a na 2 a matsayin wata jaruma sabuwa da za ta zo da danne ta, sannan ta rufe ta baki daya, inda cikin lokaci kadan na zama ni ake magana.
An ce da furodusa za ki zama?
Gaskiya abin da na so in fara da shi ke nan. Amma duk da kasancewar ina da tsohon mijina Adamu, wanda na san zai taimaka min a duk abin da nake bukata, amma ba na son in fara abin da ba ni da masaniya sosai a ciki.
Don haka na fi so in fara zama jaruma, in san yadda ake gudanar da lamarin, sannan in fara shirya fina-finai.
Haka ma ina da sha’awar zama darakta domin abokaina suna fada min cewa zan yi kyau da darakta saboda a lokuta da dama idan a kalli fim, nakan gano kura-kurai da dama cikin sauri.
Wane sauyi kike so ki kawo a masana’antar?
Ni wata irin mata ce da duk abin da nake yi, nakan yi shi da zuciya daya. Ko lokacin da muke rawa, ina yi iya yina ne.
Duk abin da za ka yi domin ka birge masu kallo, dole ka yi da kyau.
Burina in nuna kwazo da jajircewa domin kawo wa masu kallo wani sabon salon da ba su yi tsammani ba.
Da yardar Allah za su ga abin da ba su yi tsammani ba.
Za ki iya fitowa a fim daya tare da Adam A. Zango?
Lallai duk wanda zai shirya irin wannan fim din, dole sai ya tara kudi sosai.
Ni da Adamu mun yi soyayya sosai, muka yi aure kafin muka rabu, amma har yanzu muna mutunci sosai.
Amma wannan fim din, zai kasancea na daban wato zai zama zakaran gwajin dafi, domin masu kallo za su ga fim, amma kamar da gaske saboda za mu yi abin da muka saba yi ne da gaskiya kuma muka san abin da muke bukata a tsakaninmu.
Don haka zai zama fim, amma kamar da gaske.
Mene ne burinki na shiga fim?
A wajena, fim ba wai batun rawa da waka ba ne.
A lokuta da dama za ga ka an gama kallon fim, amma da wuya ka samu wanda zai fada maka darasin da ya koya.
Wasu kuma suna shiga fim ne domin su samu daukaka, wasu kuma kudi.
Amma ni ba hakan ba ne. Alhamdulillah! Na taso cikin yalwa, inda na samu duk abin da nake bukata.
Mahaifina Manjo Janar ne na soja. Amma duk iyayena sun rasu yanzu.
Amma daga cikin burina shi ne in kara samun daukaka a duniya, sannan in daga darajar gidauniyata domin in tallafa wa al’umma.
Yanzu haka gidauniyar ta fara aiki tun tuni, inda nake taimakon marasa karfi ta hanyoyi da dama, musamman marayu.
Idan na zama fitacciya a duniya, zan yi amfani da wannan shuhurar ce wajen taimako tare da kwato wa marasa karfi abubuwansu da aka danne.
Wannan shi ne babban burina a duniya.
Me ya sa aka fi kiranki da Maman Haidar?
Saboda dana Haidar. Na fi son sunan sama da Amina.
Gaskiya ina matukar son Haidar fiye da yadda sauran iyaye suka son ’ya’yansu. Haka shi ma yake so na.
Akwai lokacin da aka fada min wai ni kyakkyawa ce, bai kamata in rika yawan kiran kaina da mama ba.
Maganar ta ban dariya matuka domin ina ganin na san zafin da na ji na daukarsa a ciki na wata tara, na yi nakuda sannan na haife shi.
Ni a wajena, Maman Haidar ne suna mafi cancanta a kira ni.
Wasu suna ganin kamar soyayyar Zango ce ta sa kike son danku?
Wasu na tunanin haka.
Ko a kwanakin baya da Adamu yake bikin ranar haihuwarsa, sai na sanya hotonsa a Instagram na taya shi murna, shi kuma ya mayar da jawabi, inda ya ce yana godiya, sai ya kira ni da uwar dansa na farko.
Nan mutane suka fara magana, har kira na aka yi a waya.
Na ce musu tsohon mijina ne fa, ba makiyi ba. Don haka tunanin mutane ne wannan.
Shi ma yana matukar son danmu Haidar domin yana yawan fada a cikin wakokinsa.
Na samu da, abin da mutane da dama suke nema ta dalilin Adamu, shi ma ya samu da na farko ta dalilina.
Sannan duk wanda ya san soyayyar uwa ga da, ba zai fada haka ba. Muna mutunci dai da Adamu.
Ba ki tunanin za a iya amfani da ke wajen yakar Zango a Kannywood?
Ya zama dole a gareni in kiyaye mutuncin Adamu. Aikina kawai zan yi, in tafi.
Ai ko don darajar danmu, ya zama dole in tsare masa mutuncinsa.
Ba na tunanin akwai wanda zai iya yin amfani da ni wajen cin mutuncinsa. Muna matukar girmama juna da shi.