✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Burina in buga wa Najeriya wasa – Jume

Rufa’i Jume (Aloda) wani matashin dan wasan kwallon kafa ne da tauraruwarsa ke haskawa a tsakanin matasan Kudancin Kaduna. Ya buga wasanni da dama da…

Rufa’i Jume (Aloda) wani matashin dan wasan kwallon kafa ne da tauraruwarsa ke haskawa a tsakanin matasan Kudancin Kaduna. Ya buga wasanni da dama da ake shiryawa a yankin tare da samun kyaututtukan dan kwallon da ya fi zura kwallaye. Ya bayyana wa wakilinmu cewa babban burinsa a harkar kwallo shi ne ya buga wa kasarsa Najeriya wasa:

Aminiya: Wane ne Rufa’i Jume?
Rufa’i: Sunana Rufa’i Jume, an haife ni a Layin Zariya a cikin garin Kafanchan shekara 17 da suka wuce.
Aminiya: Me ya ja ra’ayinka ga kwallon kafa?
Rufa’i: Tun ina karami na taso na ga yayyena kusan kowa dan kwallo ne, haka yaran unguwarmu, tun ina rakiya da haka ni ma na fara sha’awa. Na fara buga wasa ne a kulob din kananan yara da ake kira Lali United, bayan na yi kwari sai Golden Balley ta dauke ni na fara buga mata wasa inda na ciyo musu kofuna daban-daban. A yanzu kuma ni ne Kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Police Academy da ke Kafanchan.
Aminiya: Wadanne nasarori ka samu a harkar kwallon kafa?
Rufa’i: Kamar yadda na fada maka a baya na ci gasanni daban-daban da ake shiryawa a Kudancin Kaduna da suka hada da Gurara Super League da aka buga a shekarar 2013, baya ga cin kofi da muka yi, ni na zamo dan kwallon da ya fi zura kwallaye a gasar, lokacin ina da kwallaye 13. Akwai gasar kofin Zaman Lafiya (Peace and Unity Cup, 2012) na marigayi tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Ibrahim Yakowa inda muka ci karamar Hukumar Igabi a wasan karshe, kuma ni na ci su, nan ma ni na fi kowa zura kwallaye a gasar. Kwanaki uku da ba mu kofin, Gwamna Yakowa ya yi hadari ya rasu. Akwai ire-irensu da dama kamar Kofin Bishop da Kofin Shettiman Kagoro Sanatan Kaduna ta Kudu (tun kafin ya zama Sanata) da Kofin Sarkin Noma (dan Majalisar Tarayya na mazabar Jama’a/Sanga), ga su nan da yawa kamar Kofin Kwamishina da na Kansila da sauransu. A yanzu haka kuma mun je wasan karshe a gasar cin Kofin Koc Bala (tsohon kocin Nasarawa
United da kuma Super Falcons na matan Najeriya), inda muka cire Aduan FC, nan ma ni ke kan gaba wajen zura kwallaye kuma nan gaba kadan za mu buga wasan karshe.
Aminiya: Mene ne burinka a nan gaba?
Rufa’i: Ba ni da burin da ya wuce in ga ina buga wa kungiyar kwallon kafa ta kasa, wato Super Eagles wasa.
Aminiya: A karshe Wane kira kake da shi ga matasa ’yan uwanka?
Rufa’i: Kiran da nake yi ga matasa shi ne kowa da hanyar cin abincinsa don haka duk abin da mutum yake yi ya rike shi da kyau kada ya raina, don bai san me zai zama nan gaba ba, koda kwallo ne ko da wata sana’a ce.