✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Burina a samu zaman lafiya da ci gaban kasa – Bafarawa

Tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, kuma tsohon dan takarar Shugaban Kasa a Jam’iyyar PDP, Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa ya ce yanayin tabarbarewar tattalin arzikin kasar nan…

Tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, kuma tsohon dan takarar Shugaban Kasa a Jam’iyyar PDP, Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa ya ce yanayin tabarbarewar tattalin arzikin kasar nan ya taimaka wajen jefa kasar cikin wani mugun hali.

Bafarawa ya ce kamata ya yi a hada karfi da karfe wajen shawo kan lamarin ba wai a rika ganin abin a matsayin abin da ya shafi gwamnati kadai ba, inda ya ce lamarin ya wuce a sanya siyasa.

Bafarawa ya bayyana haka ne a lokacin da yake zanta wa da manema labarai a Abuja a wajen kaddamar da Gidauniyar Attahiru Bafarawa domin samar da zaman lafiya da ci gaban kasa.

Alhaji Attahiru Bafarawa ya ce saboda yadda kasar ke ciki yanzu, ya sa yake shirin hada babban gangami na musamman domin nemo asalin matsalar da samar da yadda za a magance matsalar tsaro da ta addabi Arewacin kasar nan da kasar baki daya cikin sauki.

Bafarawa ya ce duk da cewa shi dan PDP ne, yana so ne ya shirya taron a Jihar Kaduna, wadda ke karkashin APC, domin a gane cewa ba siyasa a ciki, kuma kasancewar Kaduna ta fi zama a tsakiya a yankin Arewa maso Yamma.

Da aka tambaye shi ko yaya zai yi domin a samar da kwanciyar hankali da natsuwa tsakanin mutane kasancewar a wannan lamari na satar mutane da kashe-kashe ana zargin juna, sai Bafarawa ya ce, “Wannan ne ya sa muke so mu zauna tare da kowane bangare domin jin ta bakin kowane bangare sannan a gano matsalar daga tushe domin a gano yadda za a magance matsalar baki daya.”

Ya kara da cewa asali ya kafa gidauniyar ce saboda taimakon mutane da ci gaban kasa, amma kasancewar ba a ciyar da kasa gaba sai da zaman lafiya, wannan ne ya sa yake neman yadda zai taimaka wajen bayar da tasa gudunmawar wajen samar da zaman lafiya domin a samu damar ciyar da kasar gaba.