Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ta Rufe Babban Taronta na 2020 bagatatan, bayan da wani hafsanta da ke halartar taron ya kamu da cutar COVID-19.
Shugaban Rundunar, Laftanar Janar Tukuar Buratai ya sanar da soke ragowar abubuwan da a yi a taron da ofishinsa ke gudanarwa a duk shekara, don guje wa yaduwar cutar.
- Yadda aka yi bikin nada Masu Zaben Sarki a Masarautar Karaye
- Yadda gwamnati ke leken asirin wayoyin ’yan Najeriya
- Budurwa ta banka wa masoyinta wuta don ya ki aurenta
“Sakamakon sake bullar cutar COVID-19 a Abuja a karo na biyu da kuma kamauwar daya daga cikin hafsoshin da ke halartar taron Shugaban Rundunar Sojin Kasa na 2020; An soke ragowar abubuwan da aka shirya a taron”, inji kakakin rundunar, Birgediya Sagir Musa.
Rundunar ta kuma umarci mahalarta taron da su killace kansu na tsawon kwana 14 tare da kiyaye sauran matakan kariyar cutar a tsawon lokacin domin tabbatar da yanayin lafiyarsu.
“An umarci dukkanin mahalarta taron da su killace kansu kamar yadda Gwamnatin Tarayya ta tsara domin kauce wa yaduwar COVID-19”, inji sanarwar ta ranar Alhamis 10 ga watan Disamba, 2020.
An fara taron wanda Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bude ne a ranar Litinin.
Buhari da sauran shugabanni sun halarcin taron ne ta bidiyo yayin da Mininstan Tsaro, Bashir Magashi, Buratai da sauran shugabanni suka hallara a zauren taron.