✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buratai ya jinjina wa sojoji kan murkushe Boko Haram a Marte

Shugaban Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya Laftanar-Janar Tukur Buratai ya yaba wa Sashen Sojin Sama na Rundunar Operation Lafiya Dole da suka hallaka mayakan Boko…

Shugaban Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya Laftanar-Janar Tukur Buratai ya yaba wa Sashen Sojin Sama na Rundunar Operation Lafiya Dole da suka hallaka mayakan Boko Haram a garin Marte, Jihar Borno.

Buratai ta bakin Kakakin Rundunar Sojin, Birgediya Sagir Musa a ranar Lahadi, ya je sojojin sun yi bajinta wajen tarwatsa motocin yakin Boko Haram da suka yi yunkurin kai hari a kan sansanin sojin da ke Marte.

“Shugaban Rudunar Sojin Kasa na yaba wa jarumtar dakarun, musamman sojin saman Operation Lafiya Dole da suka nuna kishin kasan da ya kai ga nasarar da aka samu.

“Yana kara kira gare su da su ci gaba da matsa kaimi wurin fatattakar Boko Haram domin ganin bayanta kungiyar da wuri a Najeriya,” inji sanarwar.

Ya kuma yaba da namijin kokarin sojojin wurin tarwatsa motocin yakin mayakan Boko Haram guda bakwai a yayin da dakarun Rundunar Operation Tura Takaibango da suka yi wa maharan kwanton bauna a wajen garin na Marte.