✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bunkasa martabar rubutu da marubutan Hausa ne burina – PRO Yusuf Dingyadi

Wane kalubale ke gabanka, a matsayinka na Jami’in Hulda da Jama’a (Arewa) na kungiyar Marubuta ta Najeriya?Wannan aikin a gare ni ba sabon abu ba…

Wane kalubale ke gabanka, a matsayinka na Jami’in Hulda da Jama’a (Arewa) na kungiyar Marubuta ta Najeriya?
Wannan aikin a gare ni ba sabon abu ba ne, don haka muhimmin aiki shi ne ganin na mayar da hankali ga samar da wata hanya da ta dace don farfado da daraja da kwarjinin marubuta. Kasancewa na dade ina cikin aikin jarida, ba matsala ko kadan a kan yadda zan iya samar da hulda da jama’a don bunkasa daraja da kwarjinin wannan kungiyar tamu ta marubuta.
Mafi rinjayen marubutan sun gano bukatar da ke akwai wajen samar da shugabannin da za su iya ciyar da kungiyar da marubuta gaba fiye da komi a zukatansu. Wannan shi ne rawar da aka taka lokacin zaben sabbabin shugabanni a Kaduna.
Mece ce alkiblar marubutan Hausa dangane da irin gudunmowar da za su bayar ga ci gaban rubutu a Arewa?
Ba shakka inda aka fito, wasu marubutanmu a nan Arewa na ganin kungiyar nan ta ANA tamkar ta ’yan Kudu ce, ko ta masu rubutun Turanci. Sakamakon haka, suka daina halartar taron kasa-da-kasa, abin da ya janyo aka fara tunanin kafa wata ta yanki, watau kungiyar Marubutan Hausa ko kuma ta Arewa. Wannan abin bai samu ba saboda rashin hadin kai da ababen masarufi na daukar nauyin tafiye-tafiye da sauran lamurra.
Zuwa yanzu wannan manufar ta wuce, don kuwa mun sake fasalta wannan tunani. Za mu janyo marubutan harshen Hausa don haduwa a wuri daya, yadda kowa zai amfana tare da bunkasa harshen. Wannan zai ba al’ummarmu dama mai yawa ga ci gaban yankin nan na Arewa da kara samar da tagomashi a kan aikin marubuta.
Marubutan Arewa sun yi sanyi a gwiwa dangane da manufofin kungiyar Marubuta ta kasa dangane da kalubale mai yawa dake fuskantar marubuta da matsalolin da ke gabansu na rashin kulawa da samun tallafi daga gwamnati, masu hannu da shuni da kamfanoni.
Ba tallafi mai yawa irin yadda ake yi a da, na tallafawa a buga littafi ko bayar da agaji wajen kaddamar da littattafan da marubuta suka rubuta ko bugawa don amfanin jama’a. Yanzu kusan kashi tamanin bisa dari na marubuta suna amfani da guminsu wajen rubutawa da buga littattafansu ba tare da samun tallafi ba, duk da yake littattafan suna da amfani ga al’umma. Sauran kashi 20 na samun tallafin da bai iya zama cikon cokali ga abin da suke bukata, lamarin da yake janyo tsaiko tsakanin marubuta da kamfanonin buga littattafan wajen fitowa.
Sai kalubalen shigowar hanyar sadarwa ta yanar gizo da yawaitar labarai da hikayoyi a shafukan karatu na Facebook da Yahoo ko WhatsApp. Sun taimaka ga rage kwarjini ko karatun littattafai da ake rubutawa.
Hakan na nufin yi wa sha’anin rubutu illa?
Idan na ce bai yi ba, ban fadi gaskiya ba. Ba ko shakka tsarin rubutu ya ja baya sosai, ana samun kwantai na wasu littattafai masu muhimmanci wadanda a da suke da tasiri da amfani ga rayuwar matasa da bunkasa tafiyarwarsu a hikimance na yau da kullum. Irin rubuce-rubucen mashahuran marubuta kamar su Abubakar Imam, Labbo Yari, Gimba Abubakar da sauran irinsu, duk sun fara bacewa a zukatun matasan yau, an koma ga tarin littattafan soyayya da ba su da wata fa’ida.
Har yanzu ana kamfar irin wadannan littattafan don kuwa rayuwar ta koma ta yanar gizo da amfani da hanyar sadarwa wadda ake karatu da yada wasu sababbin labaru marasa amfani ga zukatan al’umma. Littattafan wasanni, soyayya da annashuwa sun dauke hankalin matasa fiye da na addini ko sana’a da ci gaban kasa ko sanin hanyoyin inganta rayuwa ta yau da kullum.
Har yanzu wasu a Arewacin Najeriya ba su san manufar kungiyar Marubuta ta kasa ba. Ko yaya za ku ilimantar da su?
kungiyar Marubuta ta ANA, kungiya ce kamar sauran kungiyoyin da aka kafa da nufin samar da hadin kai da ci gaban jama’a, musamman masu manufa iri daya daga abin da suke neman samun nasararsa. Hakika tun lokacin kafa ta, kungiyar ANA, shekaru fiye da talatin da suka gabata, ta samar da ingantacciyar alkibla ga ci gaba da hadin kai na marubuta a kusan ko’ina ciki da wajen Najeriya.
Sai dai mu Arewa har zuwa yau muna da jan aiki ga sanin amfaninta, don ganin mun fadada ayyukan da aka kafa ta domin shi, musamman banagren kwarin gwiwa da hadin kai na marubuta.
Mafi rinjayen marubuta da suka fito daga Arewa ba su cika samun moriya daga ayyukan kungiyar ANA ba, sakamakon irin yadda tun da farko wasu suka dauki kungiyar zama ta yan Kudu, abin da ya sanya lokaci mai tsawo babu moriya ko ci gaba ga marubutanmu tsakaninsu da ANA.
Idan ko yanayin haka ANA ya kasance ba tare da amfanar Arewa ba, har zuwa wani lokaci a baya inda aka fara samun wasu ’yan arewa suka yi azama ciki har abin da ya kawo yau. Don haka a yau da muka karbi ragamar jagorancin ANA a nan Arewa, muna da burin gyaran wannan tafiyar da sake fasalta tsarin wanzuwar ayyukanta ga marubutanmu na Arewa.
Za mu farfado da darajar rubuce-rubucen Hausa da sauran harsuna a Arewa, ta yadda za mu iya hada wata gasa dangane da kagaggun labarai ko wasu rubuce-rubuce don baje kolinsu da manufar samar da ci gaban al’ummarmu ta Arewa.
Ta yaya za ku farfado da rubuce-rubucen ke nan?
Tun farko idan ka lura, irin aikin da manyan marubutanmu suka yi a nan Arewa, za ka ga akwai kishin harshe, kasa da hazikanci. Wasu daga cikin wadannan marubuta sun yi goggaya da sauran ’yan uwansu daga kudancin kasarnan don fitar da Hausawa kunya, a kan al’adu, addini, zamantakewa da sana’o’i, abin da ya fitar da mu ga fili har aka san mu. Dangane da hakan, idan muna fatan ci gaba, dole ne mu lura da aikin nasu, mu koyi wani abu daga aikin, mu yi masa kwaskwarima ya dace da zamani don amfanin yau da gobenmu.
Akwa marubuta da suka yi fice tun da dadewa ana amfani da littattafansu har zuwa yau a makarantun firamare, sakandare da manyan makarantun karo ilmi, don koyar da karatu; bincike da karin ilmin sanin abin da duniya take ciki; duk littattafansu sun taimaka.
Littattafai irin su Ka Koyi Karatu, Iliya dan Mai Karfi, So Aljannar Duniya, kilu Ta Jawo Bau, Karanta Ka karu da sauran irinsu. Ka ga akwai Magana Jari Ce da wasu daidaikun littattafai na Hausa da aka sanya a cikin manhajar karatu, har yanzu ana aiki da su.
kokarin da wadannan marubutu suka yi ta hanyar rubuta littafi don ilimantar da mu a cikin nishadi, addini, sana’o’i da kagaggun labarai, har ma da wakoki irinsu Wakar Najeriya ta Shehu Shagari, ba karamin aiki aka yi ba ga ciyar da harshen Hausa da Arewa gaba. Don haka marubuta na Arewa da Najeriya baki daya, ba za su iya mantawa da su ba. Aikin da marigayi Abubakar Imam ya yi har zuwa yau tamkar Shata ne, sai dai a yi kama, babu irinsa.
Akwai rubuce-rubucen adabi masu yawa da aka yi sabanin irin wadanda za ka tsinta a kasuwanninmu. Rubuce-rubuce masu manufa da tsari ga ciyar da harshen Hausa da al’adunsa gaba, irin su Turmin Danya na Ibrahim Suleiman, ’Yar Tsana na Ibrahim Sheme da sauran marubutanmu irinsu Yusuf Adamu, Ibrahim Malumfashi, Bature Gagare, dan Azumi Baba, Kabiru Assada, Hafsat Abdulwaheed, Hajiya Balaraba da wasu da aka yi na soyayya, ban dariya daga irin littattafan Ado Gidan Dabino da wasu irin haka.
Hakika akwai marubuta masu yawa daga garuruwan da jihohin Kano, Katsina, Sakkwato, Kebbi, Zamfara, Neja, Jigawa da Bauchi da suka yi rubuce-rubuce masu kayatarwa da ilimantarwa da nishadantarwa don tallata al’adu, sana’o’i da tsarin rayuwa na siyasa, soyayya, jaruntaka da sauransu. Amma abin bakin ciki, wasu ba su samu damar da suke so ga shiga cikin kasa na littattafan nasu ba.
Ke nan yanzu za a mayar da hankali ga marubutan Arewa da hajarsu don farfado da wannan aikin?
Ko shakka babu, muna tabbatar wa masu sha’awar karatun littattafan Hausa cewa manufar da muka sanya gaba a wannan kungiyar, musamman shi kansa shugaban wannan tafiyar, Malam Abdullahi Denja ita ce fito da sababbin hanyoyin bunkasa wadannan littattafan.
Ya fito fili ya nuna sha’awarsa ga wannan mukamin na shugabancin kungiayr ANA don ba marubutanmu na Arewa dama da karfin gwiwa tare da nemo hanyar gyara da inganta lamarin da ya shafi marubuta a nan Arewa da kasa baki daya.
Samun dan Arewa ya jagoranci wannan kungiyar a yanzu tun bayan marigayi Gimba, zai farfado da darajar rubuce-rubucen da ake yi a Arewa. Wannan kuwa ya danganta daga hadin kai da goyon bayan da aka samu daga mafi rinjayen marubuta ’yan Arewa da masu hannu da shuni, don wallafa littattafan da gabatar da su ga jama’a.
Gwamnatoci na da muhimmiyar rawar da za su taka ga cin ma nasarar wannan aikin na sake fasalta tsarin rubutu da ci gaban rubuce-rubuce ga al’umma a nan yankin namu na Arewa.