✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buni ya sha da kyar a yakin neman zaben APC a Mazabar Ahmad Lawan

Jami'an tsaro ne suka tseratar da gwamnan bayan fusatattun matasa sun yi ruwan tuwatsu

Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya sha da kyar a gangamin yakin neman zaben Jam’iyyar APC a mazabar Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan.

Gwamna Buni na shirin fara jawabi ga dandazon magoya baya a taron da ya gudana a garin Gashua, hedikwatar mazabar Yobe ta Arewa ne, gungun wasu matasa suka shiga antayo duwatsu da tayoyi da sauran abubuwa a kan dandamalin da yake, suna ihu, ‘ba ma yi, ba ma yi.’

Nan da nan filin ya hargitse, lamarin da ya sa cikin gaggawa jami’an tsaro suka tsere da gwamnan ta bayan fage ba tare da matasan sun ji masa rauni ba.

Aminiya ta gano cewa fusatattun matasan sun yi wa manyan baki da ke saman dandamali wannan aika-aka ne bayan Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, ya mika wa Gwamna Buni abin magana domin gabatar da jawabinsa.

Wasu majiyoyi na zargin matasan da suka tarwatsa taron magoya bayan wani dan takarar Sanatan mazabar ta Yobe ta Arewa ne.

Rikicin takarar Yobe ta Arewa

Jam’iyyar ta APC ta shiga rikicin cikin gida ne bayan da rudani da ya biyo bayan zaben dan takararta na Sanatan Yobe ta Arewa, bayan  Sanata Ahmad Ibrahim Lawan da ke wakiltar mazabar ya tafi neman takarar shugabancin kasa, inda Bashir Machina ya tsaya a gurbinsa kuma ya yi nasara a zaben dan takarar da aka gudanar da farko.

Bayan Ahmed Lawan ya gaza kai bantensa a neman takarar shugaban kasa wanda da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya lashe, sai matsala ta kunno kai game da makomar Lawan, inda magoya bayansa suka matsa don ganin Machina ya janye shi, amma Machinan ya ce ba za ta sabu ba.

A kan haka ne ya shigar da kara yana neman kotu ta hana karbe masa takara, bukatar da kotu ta amince, ta kuma tabbatar da shi a matsayin dan takara.

A gefe guda kuma APC ta gudanar da wani sabon zaben dan takarar mazabar, bisa hujjar cewa zaben da Machina yake ikirarin ya lashe haramtacce ne, saboda ba da sanin uwar jami’yyar aka gudanar da shi ba.

Ganin cewa tun farko wasu kotuna sun tabbatar da takarar Bashir Machina, sai jam’iyyar ta maka shi a kotu tana kalubalantar ikirarinsa na zama dan takararta a Yobe ta Arewa bisa dogaronsa da haramtaccen zaben dan takarar da yake ikirarin ya lashe.

A karshe dai shari’ar ta kai su har gaban Kotun Koli, wadda a makon jiya ta tabbatar da Ahmed Lawan a matsayin halastaccen dan takara, ta yi watsi da zaben da Machina ke dogaro da shi.

Su wa suka yi jifa?

Aminiya ta samu labari daga wasu majiyoyi cewa hukuncin Kotun Kolin ne ya fusata wasu bangarorin da ya kai su ga tarwatsa gangamin yakin neman zaben jam’iyyar a garin Gashua.

Sai dai kuma wasu majiyoyin sun yi zargin cewa yawancin matasan da suka yi jefe-jefen magoya bayan Ahmad Ibrahim Lawan ne.

Majiyoyin sun ce matasan sun yi hakan ne domin huce haushinsu a kan Gwamna Mai Mala Buni, saboda zargin sa da goyon bayan Bashir Machina, wanda Kotun Kolin ta kwace takara daga wajensa ta ba wa uban gidansu.

A halin yanzu dai tashin hankalin da ya faru a taron ta jefa jam’iyyar da magoya bayanta cikin juyayi tare da tunanin yadda za a kwashe a sauran yankunan jihar kasancewar yanzu ne jam’iyyar ta sa danbar yakin neman zabenta a Jihar Yobe.