✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buni ya ba iyayen marayu 400 sana’o’i

Buni ya ba wa kowane marayu 200 kyautar Naira dubu hamsain kowannensu

Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, ya umarci Ma’aikatar Samar da Ayyuka ta jihar ta ba da tallafin sana’o’in dogaro da kai ga iyayen marayu 400 a jihar.

Buni ya ba da umarnin ne a ranar Asabar yayin da ya karbi bakuncin wasu marayu 200 daga kananan hukumomi 17 na jihar.

A yayin taron, gwamnan ya ba da umarnin a ba kowanne daga cikin marayun Naira 50,000 saboda a cewarsa, sun cancanci kulawar gwamnati da ta al’umma.

“Mun yanke shawarar tallafa wa marayu da iyayensu ne domin samar musu abin dogaro da kansu ta hanyar ba su jari” in ji gwamna Buni.

Mashawarcin gwamnan kan al’amuran addini kuma mai lura da shirin tallafa wa marayu na jihar, Uztaz Babagana Malam Kyari ya jinjinawa gwamnan.

A cewarsa, wannan shi ne karo na biyu da gwamnan ya ba ba da irin wannan tallafi ga marayu.