Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar ta hanzarta kai-dauki ga manoman Kananan Hukumomin Doguwa da Tudun Wada domin dakile illar da wata tsutsa ke yi a gonakinsu.
Wannan wani yunkuri ne na Majalisar don tabbatar da an samu wadataccen abinci a daminar bana.
A wani kudirin gaggawa da dan majalisa mai wakiltar Karamar Hukumar Doguwa, Alhaji Salisu Muhammad Ibrahim ya gabatar a zauren majalisar ya ce, tsutsotsin suna barazana tare da karya manoma kasancewar duk gonar da suka shiga sai sun cinye shukar da aka yi a cikin dan kankanen lokaci.
Dan majalisar ya roki mambobin majalisar su duba wannan lamari domin daukar matakin gaggawa.
A cewarsa, rashin samun dauki a kan lokaci daga gwamnatin jihar yana iya jefa manoman a cikin mummunan hali wanda hakan ka iya shafar noman abinci a bana idan aka yi la’akari da cewa Karamar Hukumar Doguwa yanki ne da yake samar da mafi yawancin abincin da ake samu a jihar.
Wannan kudiri ya samu goyon bayan ’yan majalisa masu wakiltar kananan hukumomin Tudun Wada da Kiru inda dukkansu suka tabbatar wa majalisar cewa, sun san da labarin bullar tsutsar da irin illar da take yi a gonaki.
Sun yi tarayya wajen neman majalisar ta yi kira na gaggawa ga Ma’aikatar Gona ta Jihar a je a duba wuraren a kuma kawo agajin gaggawa domin magance tsutsar.
Bayan sauraren kudirin da kuma tattaunawa a zauren majalisar, Shugaban Majalisar, Injiniya Hamisu Ibrahim Chidari tare da amincewar majalisar inda ya yi kiran gaggawa ga Ma’aikatar Gona da Albarkatun Kasa ta Jihar, ta hanzarta kawo karshen wannan tsutsa da take barazanar hana noma a yankin.
Da yake yi wa manema labarai karin haske kan matsalar, Alhaji Salisu Ibrahim ya ce, idan ba a dauki matakin gaggawa ba, tsutsar za ta yi wa manoma illar da ba a kansu kawai za ta tsaya ba, domin za ta kawo cikas ga shirin wadata kasa da abinci da gwamnati take kokarin yi.
“Kasancewar a yanzu damina ta yi nisa a yankunan, ba abu ne mai sauki ga manomi ya sake yin wata sabuwar shuka ba, don maye gurbin shukar da tsutsar suka cinye ba.
“Abu ne na tashin hankali wanda idan ba a kula ba, komai na iya faruwa kuma kowa ya san abin da hakan zai iya jefa al’ummar kasar nan. Musamman idan aka dubi cewa ana fama da tsadar abinci ballantana kuma a samu wannan yanayi kun ga ai akwai matsala.”
Ya yi fata gwamnati ta kai musu dauki cikin gaggawa don a ceto manoman yankin daga fadawa cikin halin kakani-ka yi.