✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

BUK ta kori dalibai 27 kan satar jarabawa

Jami'ar BUK ta kori dalibanta 27 ta kuma dakatar da wasu takwas da ta samu da aikata magudin jarabawa.

Jami’ar Bayero ta Kano (BUK) ta kori dalibanta 27, ta kuma dakatar da wasu takwas da ta samu da aikata magudin jarabawa.

Jami’ar ta bayyana hakan ne ranar Lahadi cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Daraktar Sashin Jarabawa da Dauka da Adana Bayanan Dalibai (DEAR), Amina Umar Abdullahi.

Daraktar ta ce hakan ya biyo bayan zaman da majalisar malaman jami’ar ta gudanar ranar 26 ga watan Janairun shekarar 2023.

Haka kuma a cewarta matakin ya yi daidai da sashi na 20.17 (Ai, iii, iv, v, vi, vii, x da na xii) na dokar jami’ar.