✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari zai yi wa ‘yan Najeriya jawabin Ranar Damokradiyya

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai yi wa ‘yan Najeriya jawabin zagayowar Ranar Damokradiyya da safiyar Juma’a. Da misalin 7.00 na safe Buhari zai yi jawabin…

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai yi wa ‘yan Najeriya jawabin zagayowar Ranar Damokradiyya da safiyar Juma’a.

Da misalin 7.00 na safe Buhari zai yi jawabin kai tsare a karo na biyu tun bayan ayyana 12 ga watan Yuni a matsayin Ranar Damokradiyya a Najeriya.

Mai ba Shugaban Kasa Shawara kan Yada Labarai Femi Adesina, a cikin sanarwar ya ce kafafen yada labarai na iya yada jawabin shugaban kasan wanda gidan talbijin na NTA zai nuna kai tsaye.

Gwamnatin Tarayya ta riga ta sanar da ranar a matsayin hutu, tare da taya dukkan ‘yan kasa murnar zagayowar ranar wadda ake gani a matsayin gimshiki ga mulkin damokradiyya a kasar.

A cikin sanarwar hutun, Ministan Harkokin Cikin Gida Rauf Aregbesola ya taya ‘yan Najeriya a cikin gida da waje murna bisa sadaukar da kai da suka yi wajen tabbatar da dorewar damokradiyya a kasar.

Sanawar da Babbar Sakatariyar Ma’aikatar Georgina Ehuriah ta sa wa hannun ta kuma bukace su da su hada kai da Gwamnatin Shugaba Buhari domin cimma manufofin da ‘yan gwagwarmaya suka sadaukar da rayuwarsu a kai.

A 2018 ne Shugaba Buhari ya maye gurbin ranar 29 ga watan Mayu da ranar 12 ga watan Yuni na kowace shekara a matsayin Ranar Damokradiyya.

29 ga watan Mayu ita ce ranar da Najeriya ke bukin zagayowar ranar kafa Jamhuriya ta hudu wadda aka fara bikin tun a shekarar 2000.