Shugaba Buhari na shirin mika wa Majalisar Tarayya wani karamin kasafin kudi domin sayen makamai da kuma rigakafin cutar COVID-19.
Buhari ya bayyana hakan ne yayin ganawarsa da Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan da Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila ranar Litinin.
- Fada a jirgi: Okorocha bai ga komai ba tukuna —Basarake
- Buhari zai tafi London ganin Likita
- ’Yan sanda sun harbe dan Shi’a, sun jikkata wasu a Abuja
Aminiya ta gano cewa babu abin da aka ware na kudi domin yin sayayyen a kasafin kudin 2020 da Majalisar Tarayya ta amince da shi a watan Disamba.
Ahmad Lawan ya bayyana cewa bangaren Majalisa da na Zartarwa sun yi amanna cewar ya kamata a yi karamin kasafin domin shawo kan kalubalen tsaro da cutar COVID-19.
Game da shawo kan matsalar tsaro, Ahmad Lawan ya ce za a yi fitar da kudade ne domin sayen makamai da sauran kayan aikin soji.
“Shi ya sa muke jiran isowar Tucson dinmu nan ba da jimawa. Motoci masu sulke kuma za su iso daga kasar Jordan da China.
“Mun kuma yi amannar cewa ba mu da isassun kayan yaki, muna bukatar fitar da kudi siyo wa sojoji kari, saboda abu mafi muhimmanci ga kowace gwamanti shi ne tsaro rayuka sannan kula da jin dadin al’umma.”
Ya ce Majalisar Tarayya za ta amince da kudurin dokar man fetur (PIB) “zuwa karshe watan Afrilu ko tsakiyar watan Mayu.”