✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari zai yi jawabin bankwana ranar Lahadi

Buhari ya nemi yafiyar wadanda ya bata wa rai.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai gabatar da jawabin bankwana a ranar Lahadi, 28 ga watan Mayu da misalin karfe 7 na safe.

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Femi Adesina ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranar Asabar.

Ya kuma bukaci gidajen talabijin da rediyo da sauran kafofin yada labarai na zamani da su hada kai wajen yada shirin.

Buhari zai mika jagorancin mulkin Najeriya ga zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a ranar Litinin a matsayin shugaban tarayyar Najeriya na 16.

Tuni dai Buhari ya nemi gafarar wadanda ya bata wa rai.