✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari zai tafi Landan ganin Likita

Shugaba Buhari zai tafi Landan don a duba lafiyarsa kamar yadda aka saba.

A ranar Talata ake sa ran Shugaba Muhammadu Buhari zai kai ziyara kasar Birtaniya domin ganin likitocinsa da za su tabbatar da ingancin lafiyarsa.

Mai magana da yawun shugaban kasar, Mista Femi Adesina ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a daren ranar Litinin.

“Shugaba Muhammadu Buhari zai yi tafiya zuwa birnin Landan a ranar Talata, 30 ga watan Maris na 2021 don a duba lafiyarsa kamar yadda aka saba.”

“Kafin tafiyarsa, tun da sanyin safiya Buhari zai gana da Shugabannin tsaro sannan ya nufi filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja domin wannan tafiya,” in ji Mista Adesina.

Sanarwar ta ce shugaban kasar zai dawo Najeriya ne a cikin mako na biyu na watan Afrilun bana.

Shugaba Buhari dai ya shafe tsawon lokaci ba tare da tafiya ketare ba sakamakon annobar cutar Coronavirus da ta dagula al’amura.

Sai dai babu shakka a karshen shekarar da ta gabata ce shugaban kasar ya kai ziyara birnin Bamako da zummar shawo kan rikicin siyasa da ya dabaibaye kasar Mali a wancan lokaci.

Kafin barkewar annobar Coronavirus, Buhari ya yi tafiye-tafiye zuwa Landan domin ganin Likita, inda a shekarar 2017, ya kwashe fiye da kwanaki 100 yana jinyar wata cuta da ba a bayyana wa duniya ba.

Haka ya sanya aka rika hayaniya da kiraye-kirayen neman shugaban kasar ya yi murabus kan zargin ba shi da cikakkiyar lafiyar da zai iya jagorantar kasar.