✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari zai tafi Abu Dhabi don taya sabon Shugaban UAE murna

Ana sa ran dawowar shugaba Buhari a ranar Asabar

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, zai bar Abuja a ranar Alhamis zuwa kasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) don taya sabon Shugaban Kasar murna.

Babban mataimaki na musamman ga Shugaban kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu ne, ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.

Ya ce Buhari zai samu rakiyar Minista a Ma’aikatar Harkokin Waje, Zubairu Dada, Ministan Sadarwa, Isa Ali Pantami, Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Mohammed Bello da Ministan Sufurin Jiragen Sama, Sanata Hadi Sirika.

Sauran ’yan rakiyar sun hada da mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Manjo-Janar Babagana Monguno (mai ritaya) da kuma Babban-Daraktan Hukumar Leken Asiri ta Kasa, Ambasada Ahmed Rufai Abubakar.

Ya ce Buhari zai gana da sabon Shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan, domin mika ta’aziyyar rasuwar tsohon shugaban kasar, mai martaba Sheikh Khalifa bin Zayed Al Nahyan.

Shehu, ya ce shugaba Buhari zai kuma mika sakon taya murna ga sabon Shugaban Kasar, tare da sabunta dankon zumuncin da ke tsakanin Najeriya da Hadaddiyar Daular Larabawa.

“Buhari cikin sakon taya murna da ya aike wa sabon shugaban kasar UAE a baya, ya jaddada kyakkyawar alakar Najeriya da kasar, inda ya bayyana cewa hadin kan gwamnatocin biyu ya taimaka wa Najeriya wajen gano kadarori da kuma gano wasu kudade da ke da alaka da ‘yan ta’adda.

“A karkashin sabon shugabancin, Shugaba Buhari na fatan hada karfi da karfe don samar da zaman lafiya, kwanciyar hankali da ci gaban kasashen biyu.”

Sanarwar ta kara da cewa ana sa ran dawowar shugaba Buhari a ranar Asabar.