Shugaba Buhari na shirin saya wa Fadar Shugaban Kasa da wasu hukumomi da cibiyoyin gwamnati sabbin motoci na Naira biliyan 23.57 a shekarar 2023.
Shugaban ya ware Naira biliyan 23.57 domin sayen sabbin motoci ga hukumomi da ma’aikatun ne, duk kuwa da cewa a kasafin 2022 da muke ciki ya ware wa 212 daga cikinsu biliyan N22.5 na sayen sabbin motoci.
- Yadda ISWAP ta yi wa ’yan Boko Haram yankan rago
- Ambaliyar Ruwa: Peter Obi ya raba burodi 24 a matsayin tallafi
Duk da cewa bai fayyace irin motocin da za a saya ba a daftarin kasafinsa na tiriliyan N20.51 na 2023, amma ya nuna hukumomi da ma’aikatu 174 da ke shirin sayen sabbin motocin na biliyan N23.57.
Wadanda za su fi kashe kudi
Aminiya ta tattaro jerin hukumomi da cibiyoyin gwamnati da za su fi kashe kudi wajen sayen sabbin motoci a 2023 kamar haka:
- Hukumar NDLEA — Biliyan N2
- Fadar Shugaban Kasa — Biliyan N1.9
- Rundunar Sojin Kasa — Biliyan N1.2
- Hukumar NAFDAC — Miliyan N946.5
- Hukumar Binciken Hatsari (AIB) — Miliyan N736.5.
- Hukumar Binciken Tsaro (DIA) — Miliyan N663
- Cibiyar Rajistar Jami’an Lafiyar Al’umma — Miliyan N616.3
- Ma’aikatar Kudi da Kasafi — Miliyan N565.1
- Hukumar Lafiya a Matakin Farko —Miliyan N540
- Sakataren Gwamnatin Tarayya —Miliyan N497.4
- Makarantar Hafsoshin Soji (NDA) — Miliyan N485
- Cibiyar Yaki da Ta’addanci — Miliyan 413.2
- Ma’aikatar Ayyuka da Gidaje — Miliyan N376
- Hukumar Gidajen Yari — Miliyan N348.4
- Kotun Gasanni da Kare Masu Sayayya —Miliyan 300
- Jami’ar Ilori — Miliyan N300
- Kwalejin Kimiyyar da Kere-kere ta Damaturu, Jihar Yobe — Miliyan N290
- Kwalejin Kimiyyar da Kere-kere ta Shendam, Jihar Filayo —Miliyan N287.7
- Hukumar Binciken Yanayi (NiMET) — Miliyan N280 million.
- Hukumar Shige-da-fice —Miliyan N276
- Ma’aiaktar Lafiya —Miliyan N273.2.
Wannan mataki ya haifar da damuwa, ganin cewa fiye da rabin cibiyoyin gwamnati da za a saya wa sabbin motocin, su ne suka samu kaso mai tsoka na kudaden sayen sabbin motoci a kasafin 2022.
Al’adar karkatar da motocin gwamnati
Hakan ya kuma haifar da damuwa, ganin cewa wasu jami’an gwamnati kan karkatar da wasu daga cikin motocin da gwamnati ke kashe biliyoyin Naira a kansu zuwa na kashin kai ko ma su yi layar zana ba tare da an dawo da su ba.
A shekarun baya-bayan na kuma, manyan jami’an gwamnati kan yi wa kansu gwanjon motocin a farashin da bai taka kara ya karya ba, idan suka tashi barin kujerusu a lokacin ritaya ko sauyin wurin aiki.
A shekarar 2021 Majalisar Dokoki ta Kasa ta kalubalanci Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya kan wasu motoci 55 da suka yi layar zana a ma’aikatar.
Ofishin Mai Binciken Kudi na Ƙasa ya shaida wa Majalisar cewa duk kokarin da ya yi na ganin an kawo motocin domin tabbatar da halin da suke ciki ya faskara.
Hasali ma ba a san inda motocin suka shige ba.
Karancin kudin manyan ayyuka a kasafi
Akwai kuma damuwa game da kason da muhimman ayyuka ke samu a kasafin da shugaban yake gabatar wa Majalisa, a yayin da Najeriya ke fama da karancin kudaden shiga, yawan cin bashi da kuma gibi da ake samu wajen aiwatar da kasafi.
Tun da Buhari ya hau mulki a 2015 yake yin kasafi mai gibi, wanda sai an ciyo bashi ake iya aiwatarwa.
Bugu da kari, ayyukan yau da kullum ke daukar kaso mai tsoka na kasafin shugaban, wanda ke da’awar tsantsaini da kuma yaki da rashawa.