Shugaba Buhari zai koma Landan inda zai shafe mako masu masu zuwa.
Kakakin Shugaban, Femi Adesina ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwar ranar Litinin.
- ’Yan IPOB na kokarin kawo cikas a kotun da ake shari’ar Kanu
- Bullar Cutar Kwalara A Najeriya: Me Ya Kamata Ku yi?
Ya ce shugaban zai fara halartar wani taro ne a birnin na Landan, sannan daga bisani ya wuce don ganin likitocinsa.
“Yau Litinin, 26 ga watan Yulin 2021, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai tafi kasar Birtaniya domin halartar taron kasa da kasa kan harkar ilimi (GPE) na 2021 zuwa 2025.
“Taron, wanda aka shirya shi a matsayin na hadin gwiwa tsakanin Firaministan Burtaniya, Boris Johnson da Shugaban Kenya, Uhuru Kenyatta zai tattara shugabannin kasashen duniya da masu ruwanda tsaki da ma shugabannin matasa domin tattaunawa kan sabbin dabarun inganta ilimi tsakanin kasashe mambobin gamayyar.
“Taron zai kuma bayar da dama ga shugabannin su bullo da nagartattun shirye-shirye na tsawon shakara biyar don inganta ilimi a cikin kasashe sama da 90.
“Kazalika, shugaba Buhari zai tattauna da Firaminista Boris Johnson kan alakar Najeriya da Burtaniya.
“Bayan kammala taron kuma, Buhari zai shafe wasu ’yan kwanaki don ganawa da likitocinsa, kamar yadda aka tsara yi a kwanakin baya.
“Muna sa ran dawowarsa a cikin mako na biyu na watan Agustan 2021,” inji sanarwar.
Yayin tafiyar, Shugaban zai sami rakiyar Ministan Harkokin Waje, Geoffrey Onyeama, Minista a Ma’aikatar Ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba, mai ba Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Tsaro, Babagana Monguno da kuma shugaban Hukumar Leken Asiri ta Najeriya, Ambasada Ahmed Rufai Abubakar.