✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari zai kai ziyarar kwana uku kasar Turkiyya

A lokacin ziyarar Buhari zai halarci taron hadin gwiwar kasashen Afirka da Turkiyya a Santambul

Shugaba Buhari zai kai ziyarar aiki kasar Turkiyya a ranar Alhamis domin halartar taron hadin gwiwar kasashen Afirka da Turkiyya.

Shugaban Kasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, shi ne zai jagoranci taron, wanda shi ne karo na uku da zai gudana a birnin Santanbul, domin yin duba kan alakar da ke tsakanin bangarorin a kawancen da suka kulla tun daga 2014.

Fadar Shugaban Kasa, ta bakin kakakin Shugaban Kasa, Garba Shehu, ta ce, Buhari zai yi tafiyar ce tare da mai dakinsa, Aisha Buhari.

Sauran ’yan rakiyar sun hada da Ministan Harkokin Waje, Geoffrey Onyeama; Ministan Tsaro, Manjo-Janar Bashir Magashi (ritaya); da Mashawarcin Shugaban Kasa kan Tsaro, Babagana Monguna.

Ministan Abuja, Mohammed Bello; Ministan Lafiya, Osagie Ehanire; Ministan Ayyukan Noma, Mohammed Abubakar; da na Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Adeniyi Adebayo; da Daraktan Hukumar Tara Bayanan Sirri, Ahmed Rufai Abubakar, na daga cikin tawagar shugaban kasar.