✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari zai kaddamar da kasafin kudi ranar Talata

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kaddamar da  kasafin kudi na badi a gaban ‘yan Majalisar Dattawa da Wakilai. A wata wasika da Yakubu Dogara ya…

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kaddamar da  kasafin kudi na badi a gaban ‘yan Majalisar Dattawa da Wakilai.

A wata wasika da Yakubu Dogara ya karanta a ranar Alhamis, Buhari ya bukaci ‘yan majalisun da su hadu a waje daya domin ya samu damar gabatar musu da kasafin kudin. Kuma wasikar ta nuna cewa shugaba Buhari zai kaddamar da kasafin kudin ne a ranar Talata 7 ga watan Nuwamba 2017 da misalin karfe biyu na rana.