✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari zai gabatar da kasafin kudin 2022 ranar Alhamis

Majalisar ta bukaci Kwamitinta na Kudi ya gabatar mata da rahotonsa ranar Laraba.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai gabatar wa Majalisar Dokoki ta Kasa da kudurin kasafin kudin 2022 a ranar Alhamis.

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijai, Sanata Ovie Omo-Agege, ne ya bayyana hakan a ranar Talatar a zauren majalisar.

“Za ku gabatar mana da rahotonku zuwa gobe (Laraba0, don ba mu damar nazartar gabatar da kasafin kudin a ranar Alhamis,” inji Omo-Agege.

Ya bukaci kwamitin harkokin kudi na majalisar da ya gaggauta aikin da yake yi kan tsare-tsaren kasafin, domin gabatar da rahotonsa a gaban majalisa zuwa ranar Laraba.

Bayan karanta takardar da Shugaban Kasar ya aike wa majalisar, shugabanta, Sanata Ahmad Lawan ya mika ta ga kwamitinin kasafin kudi.

%d bloggers like this: