✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari zai bar Najeriya fiye da yadda ya same ta —Fadar Shugaban Kasa

Ya ce Najeriya ta inganta a karkashin buhari fiye da a 2015

Fadar Shugaban Kasa ta ce a fannin tsaro da habaka tattalin arziki, Shugaba Muhammadu Buhari zai bar Najeriya fiye da yadda ya same ta a 2015.

Kakakin shugaban, Femi Adesina, ne ya bayyana hakan lokacin da yake tattaunawa da gidan talabijin na Channels ranar Talata.

Ya kuma karyata zargin da ake yi na cewa a tsawon mulkin Buhari na shekara takwas, ya nuna kabilanci wajen nadin shugabannin hukumomin tsaro.

A cewarsa, nadin nasu ba shi da wata alaka da addini, yanki ko kabilar da mutum ya fito, an fi la’akari da cancanta tun da dai doka ta ba shugaban ikon nada duk wanda ya ga dama.

Dangane da zargin cewa an fi kashe mutane a mulkin Buhari a kan shekarun baya duk da cewa bangaren tsaro na cikin manyan abubuwan da ya yi alakawari a kansu, Femi Adesina, ya ce ba gaskiya ba ne.

Ya ce, “Ka san cewa akwai wani rahoto da ya ce an fi samun karancin kashe mutane a 2022 a cikin shekara 12 da suka gabata a sakamakon ayyukan ta’addanci? Sanin kowa ne a Najeriya cewa alkaluman sun ci gaba da sauka a tsawon shekaru.

“Babu wanda yake son a sami asarar rai, komai kankantarsa, amma idan aka ce an sami ragi a yawan mutanen da ake kashewa a kowacce shekara, ni ina ganin abin a yi farin ciki ne.

“Buhari zai bar Najeriya fiye da yadda ya same ta a 2015, lokacin da kananan hukumomi 17 ke karkashin ’yan ta’adda. Hatta NYSC ba ta iya ba matasa masu yi wa kasa hidima horo a wadannan yankunan. Amma a yanzu fa?” In ji shi.

Gaame da tattalin arziki kuwa, Femi Adeshina ya ce gwamnatin Buhari ta fadada hanyoyin samun kudaden shigar Najeriya, ta yadda a yanzu kasar ta rage dogaro kacokam da danyen man fetur.