Shugaba Buhari ya ziyarci asibiti domin ganawa da fasinjojin jirgin kasan da aka ceto daga hannun mayakan Boko Haram da suka yi garkuwa da su.
Buhari ya ziyarci fasinjojin su 28 ne Asibitin NDA da ke Kaduna a ranar Alhamis, washegarin ranar da aka ceto su.
- An tsige Omehia daga matsayin tsohon Gwamnan Ribas
- Mutum 30 sun nutse a ruwa yayin tsere wa ’yan bindiga a Zamfara
- NAJERIYA A YAU: Shin kayyade Kudaden Kamfen Zai Kawo Zabe Mai Tsafta a 2023?
Kakakin Shugaban Kasa, Garba Shehu, ya ce a yayin ziyarar, Buhari ya jinjina wa jami’an tsaro bisa ceto mutanen su 23 bayan wata bakwai a hannun ’yan ta’adda.
Daga nan ya zarce zuwa Babban Filin Jirgin Sama na Kaduna, ya koma Abuja.
Buhari ya biya ta asibitin ne bayan ya halarci bikin yaye kananan hafsoshin soji karo na 69 a NDA.
A ranar Laraba ne Hedikwatar Tsaro ta Najeriya ta sanar da ceto fasinjojin da suka hada da kananan yara da mata da kuma tsofaffi a cikinsu.
A ranar 28 ga watan Maris ne ’yan bindiga suka kai harin bom kan jirgin kasan da ke hanyar zuwa Kaduna daga Abuja, suka kashe mutane sannan suka yi garkuwa da wasu.