Shugaban Muhammadu Buhari, ya yi wa malaman makaranta karin albashi da yawan shekarun aiki daga 35 zuwa 40.
Buhari ya bayyana hakan ne a wajen taron zagayowar Ranar Malamai ta Duniya ta 2020, ranar Litinin, a Abuja.
Shugaban kasar, wanda Ministan Ilimi, Adamu Adamu ya wakilta ya umarci ministan da ya tabbatar an aiwatar da sabon tsarin albashin, domin kara wa malaman kwarin gwiwar gudanar da ingantacen aiki.
Kawo yanzu dai ba a san yadda tsarin zai kasance ba.
A saurari karin bayani.