✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya yi wa Majalisa raddi kan hafsoshin tsaro

Fadar shugaban kasa ta ce Shugaban Kasa Muhamnadu Buhari ne kadai ke da dama da kuma hurumin ci gaba da aiki da manyan hafsoshin tsaro…

Fadar shugaban kasa ta ce Shugaban Kasa Muhamnadu Buhari ne kadai ke da dama da kuma hurumin ci gaba da aiki da manyan hafsoshin tsaro ko ya dakatar da su.

Mai taimaka wa shugaban kan harkokin yada labarai, Femi Adesina shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata

Sanarwar martini ne ga kiran da Majalisar Dattawa ta yi ga shugaban kan ya kori manyan hafsoshin tsaron.

Adesina, a cikin martanin mai take “Manyan hafsoshin tsaro: Matsayin fadar shugaban kasa shawarar Majalisar Dattawa”,  ya ce shugaban zai yi duk abin da ya san zai haifar wa kasar da mai ido.

“Fadar Shugaban Kasa ta saurari sakon Majalisar kuma tana kara jaddada musu cewa ikon nadawa ko sauke manyan hafsoshin tsaro alhaki ne da ya rataya a wuyan Shugaban Kasa.

“A matsayinsa na Babban Kwamandan Askarawan Najeriya, zai yi duk abin da ya san zai haifar wa da kasar da mai ido a kowane lokaci”, inji sanarwar.

A ranar Talatar Majalisar Dattawa ta bukaci manyan hafsoshin tsaron kasar da su sauka daga mukamansu saboda abin da Majalisar ta kira gazawarsu a bangaren tsaro bayan da Sanata Ali Ndume (Borno, APC) ya gabatar bukatar hakan a gaban majalisar.