Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya aike da sakon ta’aziyyarsa ga gwamnati da kuma daukacin al’ummar kasar Zambiya kan rasuwar tsohon shugaban kasar, Rupiah Bwezani Banda.
Banda ya rasu yana da shekara 85 a duniya.
- Martani: Rasha ta sanya wa Amurka takunkumi
- Har yanzu Manchester City ba tsarar Liverpool ba ce —Bernardo Silva
Sakon na cikin wata sanarwa da hadiminsa kan kafafen watsa labarai, Garba Shehu ya fitar a ranar Talata, zuwa ga Shugaba Hakainde Hichilema na Zambiya.
Buhari ya bukaci shugabanni a Afirka su yi koyi da kyawawan halaye irin na marigayi shugaba Banda wajen martaba tsarin dimokuradiyya.
Shugaba Banda ya sauka daga mulki a 2011 sannan ya jagoranci mika mulki a kasar a 2021.
Buhari ya yi addu’ar samun ci gaba da waraka daga rashin shugaba Banda ga iyalansa.
An shirya bikin binne gawar Mista Banda a ranar 17 ga watan Maris, 2022.