✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari ya yi ta’aziyyar mutuwar Farfesa Adetokunbo Lucas

Farfesa Lucas ya rasu yana da shekaru 89 a duniya.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aike da sakon ta’aziyyarsa ga ’yan uwa da abokan arziki na marigayi Farfesa Adetokunbo Oluwole Lucas, wanda ya rasu yana da shekaru 89.

Buhari ya aike da sakon ne ta hannun mai magana da yawunsa, Mista Femi Adesina a ranar Litinin.

Bayan samun labarin rasuwar Farfesa Lucas, Shugaba Buhari ya ce duniya ta yi rashin gwarzo a fannin kiwon lafiya.

Buhari ya jinjina wa marigayin, bisa irin gudunmawar da ya bayar a fannin harkar kiwon lafiya.

Kafin rasuwarsa, Farfesa Lucas ya rike mukamin Shugaban Sashen Yaki da Cututtuka a Jami’ar Ibadan kuma Shugaba a Kungiyar Bincike ta Likitoci.

Buhari ya ce Farfesa Lucas sunansa bai tsaya iya Najeriya domin kuwa ya ratsa ketare, inda ya kawo sauye-sauye lokacin da ya rike mukamin Daraktan Bincike da Horaswa na Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO).

Shugaba Buhari ya roki dalibai masu tasowa da su yi koyi da marigayin, sannan su dora daga irin harsashin da ya kafa a rayuwa.

 

%d bloggers like this: