✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari ya yi bankwana da ministocinsa 10

Sai dai daga bisani Chris Ngige ya yi mi’ara koma baya

Biyo bayan umarnin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na ajiye aiki ga duk Ministan da ke son tsayawa takara a zaben 2023, yanzu haka Ministoci 10 sun yi bankwana da kujerunsu bayan ajiye aiki.

Ministan Yada Labarai da Al’adu, Lai Mohammed ne ya ba da sanarwar a ganawarsa da ’yan jarida bayan kammala taron bankwana da Ministocin da aka gudanar a Fadar Gwamnati da ke  birnin tarayya Abuja.

Kazalika Ministan ya ce Shugaba Buhari ya ce nan ba da jimawa ba za a maye gurbinsu da wasu sababbi.

Lai Mohammed ya ce daga cikin wadanda suka halarci taron akwai Ministan Sufuri, Rotimi Ameachi, da na Neja Delta, Godswill Akpabio, sai na Kwadago, Chris Ngige, da na Kimiyya da Fasaha, Ogbonnaya Onu, sai na Man Fetir, Temipre Sylva.

Sauran sun hada da Ministar Mata Paulin Tallen, da Uche Ogar na Ma’adinai, sai na Shari’a, Abubakar Malami da kuma na Ma’aikatar Ilimi, Emeka Nwajiuba wanda ya ba da uzurin rashin  samun halartar taron.

Wasu daga cikin ministocin dai sun sayi fom din takarar Shugabancin Kasa, ko na Gwamna,  yayin da wasu kuma suka sayi na ’yan majalisa duk dai karkashin inuwar jam’iyar ta APC.

Sashi na 84 na kundin dokar zabe da ke tada kura ya bayyana cewa babuwani mai mukamin siyasa da zai rike daliget ko a zabe shi a babban zabe na kowacce jam`iya a matsayin dan takarar kowanne irin zaben.

Hukumar zabe ta kasa INEC ta dai bawa jam`iyu  wa`din mika sunayan yan takarasu zuwa ranar 3 ga watan YUNIN 2022.

Sai dai daga bisani Ministan Kwadago, Chris Ngige ya yi mi’ara koma baya, inda ya ce ya fasa takarar, zai ci gaba da rike mukaminsa na Ministan.