Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da yunkurin juyin mulki da wasu sojoji suka yi a kasar Guinea-Bissau.
Shugaba Buhari ya tattauna da Shugaban Kasar Guinea-Bissau, Umaro Embalo a ranar Talata, bayan tsallake rijiya da baya da ya yi kan juyin mulkin, wanda bai yi nasara ba.
- Buhari zai tafi Habasha taron AU ranar Alhamis
- ’Yan bindiga sun hallaka mutum 40 a sansanin ’yan gudun hijirar kasar Kongo
Cikin wata sanarwa da kakakin Shugaban Kasa, Malam Garba Shehu, ya fitar a ranar Laraba, ya ce Buhari ya taya Shugaban na Guinea-Bissau murna kan tsira da ya yi game da juyin mulkin da aka yi yunkurin yi masa, inda ya jinjina wa dakarun sojin da suka tsaya tsayin daka wajen kare Shugaban.
Buhari ya kuma yi tir da yunkurin inda ya ce gwamnatin Najeriya za ta taimaka wa gwamnatin shugaba Embalo na kasar Guinea-Bissau.
Embalo, yayin zantawarsa da Buhari wayar tarho, ya ce komai ya daidaita a kasar kuma al’amura sun koma yadda suke bayan yunkurin yi masa juyin mulki.