✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari ya yi Allah-wadai da kisan shugaban APC na jihar Nasarawa

Shugaba Buhari ya mika sakon ta'aziyyarsa ga iyalan mamacin.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da kisan da ‘yan bindiga suka yi wa shugaban APC a jihar Nasarawa, Philip Shekwo.

Buhari ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu ya fitar ranar Lahadi, inda ya ce dole ne a kawo karshen ayyukan ‘yan bindiga.

Shugaban ya amince da shawarar Babban Sufeton ‘Yan Sanda na kasa Mohammed Adamu na kara aike wa da jami’an tsaro zuwa jihar.

Shugaban kasa ya jajanta wa iyalan Shekwo bisa rashinsa, inda ya bayyana marigayin a matsayin dan kasa na gari.

Rahotanni sun bayyana cewa an harbe marigayin har sau biyu ne wanda hakan ya yi sanadin rasa ransa da safiyar Lahadi, kwana daya bayan ‘yan bindiga sun sace shi daga gidansa a Lafiya.

Ya zuwa yanzu dai jami’an tsaro na ci gaba da bincike don gano hakikanin wadanda suka hallaka shi.