Shugaba Muhammadu Buhari ya taya Shugaba Nana Addo Dankwa Akufo-Addo na kasar Ghana, murnar sake lashe zaben kasarsa a karo na biyu.
Shugaba Buhari cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa Mallam Garba Shehu ya fitar a ranar Alhamis, yay aba wa mutanen Ghana kan hadin kan da suka bayar wajen ganin an kammala zaben shugaban kasar da ‘yan majalisa cikin lumana da kwanciyar hankali.
- An killace Buratai bayan COVID-19 ta kashe Janar din soja
- Coronavirus ta kama karin mutum 675, ta kashe 6 a Najeriya
- An kama mutum 2 da suka yi garkuwa da ba’Amurke a jihar Sakkwato
Shugaban kasar ya ce wannan shi ya kara tabbatar da madaidaiciyar hanyar shugabanci a bisa tafarki na siyasa da kuma samun gindin zama da tsari na dimokuradiyya ya yi a Yammacin Afrika.
Ya kuma yi kira ga sauran ’yan takarar da su rungumi kaddara tare da yin riko da akida ta kishin kasa fiye da komi domin tabbatar da zaman lafiya yayin da kuma ya ba da shawara da su nemi warware duk wasu korafe-korafe ta hanyar da doka ta tanada.
Buhari wanda ya tabbatar da akwai kyakkyawar alaka tsakanin tsakanin Najeriya da Ghana ta tsawon shekaru aru-aru, ya ce yana fatan yin aiki tare da takwarsansa na Ghana domin cimma burin da aka sa a gaba wanda zai kawo zaman lafiya, ingancin tsaro da kuma wanzuwar kasashen biyu da kuma Afrika baki daya.
Buhari ya yi wa Shugaba Akufo-Addo fatan samun nasara a sabon wa’adin mulkin, tare da fatan samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasarsa gami da inganta dangartakar kasashen biyu.