✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari ya taya Manjo Janar Bajowa murnar cika shekaru 80

Shugaban kasa Muhamamdu Buhari da Janar Bajowa sun yi aiki tare a lokacin mulkin Soji.

Shugaba Muhammadu Buhari ya taya tsohon Sakataren Ma’aikatar Tsaro ta Kasa, Manjo Janar Oluyemi Joseph Bajowa (mai ritaya) murnar cika shekaru 80 a duniya.

Buhari ya aike da sakon taya murnar tasa ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa Malam Garba Shehu ya fitar a ranar Litinin.

Shugaba Buhari ya taya Manjo Janar Bajowa murna tare da ’yan uwansa da abokan arziki da kuma al’ummar Jihar Ondo baki daya.

Buhari ya ce ya tuna lokacin da suka yi aiki da Janar Bajowa, a lokacin mulkin Soji a Maiduguri.

Sanarwar ta ce, “Ni da Bajowa mun yi aiki tare, lokacin ina jagorantar Hukumar rarar man fetur ta PTF, shi kuma Bajowa yana aiki matsayin Sakataren Ma’aikatar Tsaro ta Kasa.”

Shugaba Buhari ya yi wa Manjo Jajar Bajowa fatan alheri, son barka da kuma kasancewa cikin koshin lafiya.