✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari ya taya Macron murnar lashe zaben Faransa

Ya ce alaka ta kara karfi tsakanin Faransa da Najeriya tun bayan darewar Macron mulki

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya taya takwaransa na kasar Faransa, Emmanuel Macron murnar lashe zabe a karo na biyu.

Shugaban ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Garba Shehu, ya fitar ranar Litinin, inda ya ce shugaba Macron ya kafa tarihi wajen Shugaban Kasa na farko da ya mulki kasar a jere a tsawon shekaru.

Shugaba Buhari ya bayyana yadda takwaran nasa na Faransa ya shafe wata shida a Najeriya, inda ya yi aiki da Ofishin Jakadancin Faransa na Najeriya a 2002, wanda ya ce kwarewarsa za ta tallafa wa matasa masu tasowa.

Kazalika, Buhari ya bayyana yadda alaka ta kara karfi tsakanin Najeriya da Faransa tun bayan darewar Macron kan mulki a 2017, sannan kuma ya ziyarci Najeriya a 2018.

Ya ce, sabon zababben Shugaban Kasar, ya yi nasarar kirkiro hanyoyin habaka tattalin arziki, al’adu da kuma harkar tsaro a tsakanin Najeriya da Faransa, a taron kasashen Afirka da aka yi a 2020 a Faransa.

Buhari ya kuma taya Shugaban da mai dakinsa, Brigitte Macron, da sauran abokan tafiyar siyasarsa kan wannan nasara da suka yi.

Ya jadadda wa shugaba Macron Najeriya za ta ci gaba bai wa kasarsa goyon baya da hadin kai, wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaban al’umma.

Buhari ya yi wa Macron fatan nasara da tallafin Ubangiji wajen sauke nauyin da ya hau kansa a karo na biyu.

%d bloggers like this: