Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya Gwamna Rotimi Akeredolu murnar lashe zabe a matsayin gwamnan jihar Ondo a wa’adi na biyu.
Shugaban kasar ya taya Mista Akeredolu murna cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi ta bakin mai magana da yawunsa, Mista Femi Adesina.
A yau Lahadi ne dai Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta sanar cewa Gwamnan Jihar Ondo Rotimi Akeredolu ne ya lashe zaben gwamna da aka gudanar a ranar Asabar.
Shugaban Jami’ar Ibadan, Farfesa Abel Idowu Olayinka, wanda shi ne Babban Bature zabe na INEC, yayin bayyana sakamakon zaben a ranar Lahadi ya ce Akeredolu ya samu nasara ne da kuri’a 292,830.
Alkaluman sun nuna Akeredolu da ke neman wa’adin mulki na biyu a jam’iyyar APC ya samu gagarumar rinjaye a 15 daga cikin Kananan Hukumomi 18 na jihar.
Babban abokin hamayarsa, Eyitayo Jegede na jami’ar PDP ya samu kuri’a 195,791 a matsayi na biyu a zaben.
Mataimakin Gwamnan, Agboola Ajayi wanda ya yi takara a karkashin jam’iyyar ZLP shi ne ya zo na uku bayan ya samu kuri’a 69,127.