Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya fara ziyarar aiki ta kwanaki biyu a Jihar Katsina.
A yayin ziyarar, Buhari zai kaddamar da wasu ayyuka da Gwamna Aminu Masari ta aiwatar.
- Copa Del Rey: Barcelona ta tsallaka matakin kusa da na karshe
- Rundunar ‘Operation Hadin Kai’ ta kashe mayakan ISWAP 23 a Borno
Wasu daga cikin ayyukan sun hada da kofar-Kaura da gadar kasa ta Kofar Kwaya, Gidan Tattara Kudaden shiga na Katsina, da dai sauransu.
Zai kuma duba wasu ayyuka da ake gudanarwa a babban birnin na Dikko.
Buhari zai kuma kaddamar da wasu makarantu, asibitoci da tituna a ziyarar ta shi ta kwanaki biyu.
Kazalika Shugaba Buhari zai kaddamar da sabuwar masana’antar sarrafa shinkafa ta Darma, wadda hamshakin dan kasuwar nan na Katsina, Alhaji Dahiru Barau-Mangal ya kafa.
Kamfanin Dillancin Labarai (NAN), ya ruwaito cewa an girke jami’an tsaro a ciki da wajen Katsina, musamman hanyoyin da Shugaban Kasa zai bi da kuma wuraren da zai kaddamar da ayyukan.
Tuni dai rundunar ‘yan sandan jihar ta sanar da rufe wasu manyan hanyoyin na wucin gadi daga ranar Alhamis da misalin karfe 8 na dare zuwa karfe 12 na rana.
Hanyoyin sun hada da IBB zuwa Kofar Kaura, Steel Rolling Mills zuwa shatalelen Liyafa, sannan da hanyar Jami’ar Al-Qalam zuwa Kofar Kaura.