✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya sanya hannu a kan kasafin 2021

Ya sa hannu a kan kasafin tiriliyan N13.58 na 2021 awanni kafin shiga sabuwar shekarar

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a kan kasafin kudin Najeriya na 2021 awanni kadan kafin shiga sabuwar shekarar.

Shugaban Kasar ya sanyan hannu a kan kasafin na Naira tiriliyan 13 da bilyan 588 ne da safiyar Alhamis, 31 ga Disamba, 2020, kwana uku bayan Majalisar Tarayya ta mika masa da shi.

Buhari ya sanya hannun ne a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja, kwana 10 bayan Majalisa ta kammala aiki a kan kasafin da ya faraz gabatar mata a ranar 8 ga watan Oktoba.

Kasafin ya ware Naira tiriliyan 4.125 domin manyan ayyuka, tirilyan N5.641 na kanan ayyuka, biliyan N496.528 domin hukumomin gwamnati da kuma tiriliyan N3.324 na biyan basuka.

Yayin aikin da ta kammala ranar 21 ga watan Disamba a kan kasafin, Majalisar Tarayya ta kara Naira biliyan 505 a kan adadin da Buhari ya fara gabatar mata.

Hakan ya sa kasafin ya karu daga Naira tiriliyan 13.082 da Buhari ya gabatar zuwa tiriliyan N13.588 da aka rattaba wa hannu.

Shugabannin Majalisar Tarayya da kwamitocinsu na kasafi tare da ’yan Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) na daga cikin mahalarta zaman na ranar karshe a shekarar 2020.