✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari ya nada sabbin Manyan Hafsoshin Tsaro

Buhari ya sanar da nadin sabbin Manyan Hafsohin Tsaro

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nada sabbin Manyan Hafsoshin Tsaron Najeriya.

Maye gurbin Manyan Hafososhin Tsaron tamkar wata bazata ce, kasancewar  kwararru da sauran jama’ar Najeriya sun jima suna kiran Buhari ya nada sabbin jini, saboda gazawar manyan hafsoshin.

Sanarwar da kakakin Shugaban Kasa, Femi Adeshina ya fitar a ranar Talata, ta ce Buhari ya yi sabbin nade-naden ne bayan amincersa da ajiye aiki da kuma ritayar Manayn Hafsoshin Tsaron.

Sabbin Hafsoshin Tsaro

Sabbin Manyan Hafsohin tsaron su ne Manjo-Janar LEO Irabor a matasayin Babban Hafsan Hafsoshi, wanda zai maye gurbin Janar Abayomi Gabriel Olanisakin.

Sabon Shugaban Rundunar Sojin Kasa kuma shi ne Manjo-Janar Ibrahim Attahiru wanda zai maye gurbin Laftanar Janar Tukur Buratai.

Air Vice-Marshall IO Amao shi ne sabon Shugaban Rundunar Sojin Sama kuma maganin Air Marshal Sadiqu Baba Abubakar.

Shugaban Rundunar Sojin Ruwa na yanzu shi ne Rear Admiral AZ Gambo bayan an sauke Admiral Ibok Ete Ibas.

Sanarwar ta ce Buhari ya yaba wa tsoffin Manyan Hafsohin Tsaron bisa “manyan nasarorin da suka samu wajen samar da zaman lafiya a kasarmu” sannan ya yi musu fatan alheri.

Ya kuma taya sabbin wadanda aka nada murna tare da kiran su da su zama masu kishin kasa da jajircewa wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansu.

Shin Buhari ya amsa kira ne?

Wasu dai na ganin hakan tamkar Shugaban Kasar ya amsa kiraye-kirayen da ake yi masa na nada sabbin jini su jagoranci rundunonin soji, domin yakar matsalar tsaro da ta addabi kasar nan.

Idan ba a manta ba, bayan ‘yan bindiga sun sako dalibai 344 da aka yi garkuwa da su a Kankara, Jihar Katsina, Buhari ya bayyana damuwa game da matsalar tsaro a Najeriya, ya kuma ce zai yi sauye-sauye a bangaren tsaro a shekarar 2021.

“Matsalar tsaro ta dame ni matuka kuma ina fatan shekara mai zuwa (2021) za a samu sauyi.

“Shugabannin tsaro da za su ci gaba da aiki, sai aiki ya yi musu yawa; Muna da jan aiki a gabanmu” kamar yadda ya bayyana a wata hira inda ya ce ba zai yi karin bayani ba saboda yanayin tsaro.

A jawabinsa na sabuwar shekara Buhari ya bayyana aniyarsa na yin “yin gyara da sauya dabara”, a bangaren tsaro.