Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sake nada Jelani Aliyu a matsayin shugaban Hukumar Bunkasa Kirkira da Zane-zane ta Kasa (NADDC) a karo na biyu.
Sanarwar nadin nasa na kunshe ne a wata wasika mai dauke da kwanan watan bakwai ga watan Afrilun 2021, dauke da sa hannun Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Muhstapha.
Idan za a iya tunawa, a watan Afrilun 2017, Shugaba Buhari ya nada Jelani wanda a lokacin ke aiki da fitaccen kamfanin kera motocin nan na Amurka wato General Motors don ya shugabanci NADDC.
Ya dai yi fice ne wajen zana motocin da suka kara fito da kimar kamfanin a idon duniya bayan shafe sama da shekaru 100, tare da samar masa da alkibla ta hanyar zana mota kirar Chevrolet Volt mai aiki da wutar lantarki.
Shekaru hudu da nadin nasa, Jelani Aliyu ya aiwatar da sabbin manufofi a banagren kera motoci na Najeriya inda har manyan kamfanoni irinsu Dangote, Innoson, Hyundai da Honda da ma wasu da dama suka fara harhada motoci a Najeriya.
Ko a kwanakin baya dai sai da ya jagoranci kaddamar da wata motar da aka hada a Najeriya mai aiki da hasken rana.