Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya sake sabunta nadin mukamin Dokta Bello Aliyu Gusau a matsayin Babban Sakataren Hukumar Kula da Rarar Man Fetur (PTDF) da Ahmed Bobboi a matsayin Shugaban Asusun Daidaita Farashin Man Fetur (PEF).
Cikin sanarwar da mai magana da yawun shugaban kasar Mista Femi Adesina ya fitar a ranar Juma’a, ya ce an kuma sabunta nadin Injiya Simbi Wabote a matsayin Babban Sakataren Hukumar Tabbatar da Ka’ida Wajen Sayar da Kayayyakin Najeriya (NCDBM).
Adesina ya ce sabuntar nadin ta biyo bayan shawarar da Karamin Ministan Man Fetur, Timipre Sylva ya bai wa Gwamnatin Tarayya ta tsawaita wa’adin mukaman manyan jami’an sakamakon kwazon da suka yi.
A cewar sanarwar, an yaba wa Dokta Gusau da ya jagoranci Hukumar PTDF cikin nasara a tsawon shekaru hudu da suka gabata yayin da ya rike amana tare da ba da muhimmancin gaske kan wasu tsare-tsare guda bakwai da aka gabatar a watan Janairun 2017.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, an sabunta nadin Bobboi ne saboda muhimmiyar rawar da ya taka wurin kawo sauyi managarci a bangarorin samar da iskar gas da fetur da sauransu.
Ta kara da cewa, shugaban NCDMB, Wabote shi ma ya yi jagoranci mai kyau a hukumar musamman yadda ya tsaya tsayin daka wajen kammala ginin hedkwatar hukumar da sauran ayyuka da dama da suka janyo masa yabo a hukumar.