Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya yi wa dogarinsa, Laftanar Kanal YM Dodo kwalliyar anini ta karin girma da ya samu zuwa matsayin Kanal.
Hotunan da Fadar Shugaban Kasa ta yada sun nuna cewa, Buhari tare da Mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo sun sa wa Laftanar Kanal YM Dodo da a yanzu ya zama Kanal aninin ne gabanin taron Majalisar Tsaro da ya gudana a Abuja.
- Najeriya A Yau: Yadda “Ake Karo da Gawarwaki” a Jalingon Jihar Taraba
- Saif al-Islam: Hukumar zaben Libya ta haramta wa dan Gaddafi takara
Bayanai sun ce Buhari ya jagoranci taron Majalisar Tsaro ne a Fadar Shugaban Kasa ta Villa da ke Abuja a ranar Alhamis.
Wadanda suka halarci taron sun hada da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaba Kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, Mai bai wa Shugaban Kasa Shawara kan Sha’anin Tsaro, Janar Babagana Monguno da Shugaban Hukumar Leken Asiri (NIA), Ambasada Ahmed Rufa’i Abubakar.
Sauran wadanda suka halarci taron sun hadar da Babban Hafsan Sojin Najeriya, Janar Lcuky Irabor da kuma Manyan Hafsoshin Rundanar Sojojin Ruwa, Kasa da na Sama.