Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince a rika bai wa ’yan Najeriya fiffiko a kan ’yan kasashen waje wurin bayar da kwangiloli.
Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a lokacin da yake sanya hannu kan wasu takardun doka ta Shugaban kasa a fadarsa da ke Abuja a ranar Talatar da ta gabata.
“A cikin wannan doka ta Shugaban kasa, Shugaban kasa ya bayar da umarni ga hukumomi da ma’ikatun gwamnati su rika bayar da fifiko ga kamfanonin ’yan kasa wajen tsarawa da aiwatar da ayyukan tsaron kasa,” inji wata sanarwa da Shugaba Buhari ya wallafa a shafinsa na Twitter.
Ya kara da cewa ya dauki wannan mataki ne domin kara samar da ayyukan yi ga ’yan Najeriya.
Sai dai ya kara da cewa za a bai wa kamfanonin waje dama idan har kamfanonin cikin gida ba su da kwararrun da za su aiwatar da wani aiki da kwangiloli da gwamnati ke son su yi.
Shugaban kasar ya haramta wa Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida bayar da biza ga ’yan kasashen waje da za su shigo Najeriya domin gudanar da dukan ayyukan da akwai wadanda ka iya yin su a kasar nan.