✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya sa hannu a kan dokar Coronavirus

Shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a kan Dokar COVID-19 ta shekarar 2020. Mai magana da yawun Shugaban Kasa Femi Adesina ne ya bayyana hakan…

Shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a kan Dokar COVID-19 ta shekarar 2020.

Mai magana da yawun Shugaban Kasa Femi Adesina ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar da maraicen Litinin.

“Ta hanyar amfani da ikon da Sashe na 2 da na 3 da na 4 na Dokar Killace Jama’a suka ba shi, da ma sauran dokokin da suka ba shi ikon yin haka, ranar Litinin Shugaba Muhammadu Buhari ya sanya hannu a kan Dokar COVID-19 ta 2020, wadda ta ayyana Coronavirus a matsayin cutar da ke yaduwa mai hatsari”, inji Mista Adesina.

Ya kara da cewa Dokar, wadda ta fara aiki ranar 30 ga watan Maris, ta kuma samar da madogara ta shari’a ga dukkan matakan da Shugaba Buhari ya bayyana dauka a jawabinsa na ranar 29 ga wata, “ciki har da hana fita a Jihar Legas da Yankin Babban Birnin Tarayya da Jihar Ogun da sauran matakan da aka dauka don hana annobar yaduwa a kasar nan”.

Bayan haka kuma dokar, a cewar Adesina, za ta bai wa cibiyoyin kudi takaitacciyar dama ta gudanar da harkokinsu.

“Bugu da kari, don tabbatar da cewa ‘yan Najeriya za su iya aikewa da kudi ta intanet kuma za su iya fitar da su a na’urorin cire kudi (ATM) duk da hana fitar, an bai wa cibiyoyin kudi dama su yi aiki sama-sama don tabbatar da cewa komai na gudana yayin da dokar take aiki”.

Da maraicen ranar Lahadi ne dai Shugaba Buhari ya sanar da hana fita kwata-kwata har tsawon mako biyu a jihohin Legas da Ogun da kuma Yankin Babban Birnin Tarayya da nufin hana cutar COVID-19 yaduwa zuwa wasu jihohi.

Sai dai kuma a wani jawabi da ya yi ga al’ummarsa ta gidajen rediyo da talabijin, Gwamna Dapo Abiodun na Jihar Ogun ya ce dokar za ta fara aiki a yankin ne ranar Juma’a, yana mai cewa ya samu izinin jinkirta aiki da ita daga Fadar Shugaban Kasa.

Tun da safiyar Litinin ne dai mutane suka fara tururuwa suna barin Yankin Babban Birnin Tarayya don guje wa dokar.

Shugaba buhari dai ya ce daukar matakin ya zama dole saboda galibin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar a wadannan yankuna suke don haka ya zama dole a hana fita da ita zuwa wasu yankunan.