✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari ya rantsar da Ariwoola a matsayin sabon Alkalin Alkalan Najeriya 

An rantsar da shi bayan Ibrahim Tanko Muhammad ya ajiye aiki.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya rantsar da Mai Shari’a Olukayode Ariwoola a matsayin Alkalin Alkalan Najeriya na riko ranar Litinin. 

Matakin Shugaban ya biyo bayan ajiye aikin da tsohon Alkalin Alkalai, Ibrahim Tanko Muhammad ya yi a ranar Litinin, sakamakon rashin lafiya da ya yi ikirarin yana fama da ita. 

Taron rantsar da Ariwoola ya gudana ne a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.

Wata majiya ta bayyana mana cewa zai ci gaba da zaman alkalin alkalan na riko har zuwa lokacin da za a mika sunansa gaban Majalisar Dattawa domin tantance shi a matsayin cikakken alkalin Alkalan. 

Yadda Buhari ya rantsar da sabon Alkalin Alkalan Najeriya.

An dai haifi Ariwooria ranar 22 ga watan Agustan shekarar 1954 a jihar Oyo, kuma kafin ba shi wannan matsayin, ya rike matsayin Alkalin kotun daukaka kara, kafin a kara masa matsayi zuwa na kotun Koli a 2011.