✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari ya nada wa NNPC sabbin shugabanni

Shugaba Muhammadu Buhari ya ba da umarnin yi wa NNPC Limited rajista

A matsayinsa na Ministan Mai, Shugaba Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin yi wa Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPC) rajista a matsayin kamfanin kasuwanci, sannan ya nada masa sababbin shugabanni.

Bayanin hakan na kunshe ne a wata sanarwa mai dauke da sa-hannun Femi Adesina, Mashawarci na Musamman ga Shugaban Kasa a Kan Al’amuran Yada Labarai.

“Wannan ya dace da tanade-tanaden Sashe na 53(1) na Dokar Man Fetur (PIA) ta 2021, wadda ta bukaci Ministan Albarkatun Man Fetur ya bayar da umarni a yi wa NNPC Limited rajista a cikin wata shida da fara aiwatar da dokar, bayan tuntubar Ministan Kudi game da hannayen jarin Kamfanin”, inji sanarwar.

A watan Agusta ne dai Shugaba Buhari ya rattaba hannu a kan Dokar, wadda ta tanadi sauya fasalin NNPC ya koma kamfanin kasuwanci a maimakon hukuma ta gwamnati.

Don haka ne, a cewar Mista Adesina, aka umarci Shugaban NNPC, Mele Kyari, ya dauki dukkan matakan da suka dace don tabbatar da cewa an yi rajistar kamfanin kamar yadda Dokar ta tanada.

Ya kara da cewa, “Bugu da kari, a bisa ikon da Sashe na 59(2) na PIA ya ba shi, Shugaba Buhari ya amince da nadin Hukumar Daraktoci da Hukumar Gudanarwa ga NNPC Limited, wadanda za su fara aiki daga ranar da aka yi wa kamfanin rajista”.

Sababbin shugabanni

Hukumar Daraktocin, kamar yadda sanarwar ta bayyana, shi ne Sanata Ifeanyi Ararume.

Shi kuwa Mele Kolo Kyari, shi zai dare kujerar Shugaban Kamfanin (CEO), yayin da Umar I. Ajiya zai zama Babban Jami’in Kudi.

Sauran mambobin Hukumar Daraktocin su ne Dokta Tajudeen Umar (Arewa Maso Gabas), da Misis Lami O. Ahmed (Arewa ta Tsakiya), da Mallam Mohammed Lawal (Arewa Maso Yamma), da Sanata Margaret Chuba Okadigbo (Kudu Maso Gabas), da Barista Constance Harry Marshal (Kudu Maso Kudu), da Cif Pius Akinyelure (Kudu Maso Yamma).

Baya ga sayar da hannayen jarin NNPC, Dokar ta PIA ta kuma tanadi ware wani kaso daga kudin shigar da ake samu daga man fetur don al’ummomin yankin da ke samar da mai.

Sai dai tuni wasu mutanen yankin suka yi fatali da Dokar, suna korafi a kan abin da ta tanadar musu.

Da zarar an yi rajistar NNPC Limited dai, gwamnati za ta tsame hannunta daga gudanar da harkokin kamfanin.

%d bloggers like this: