Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada Dokta Pokop Bupwatda a matsayin sabon Shugaban Asibitin Jami’ar Jos.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Mataimakin Daraktan Yada Labaran Ma’aikatar Lafiya Ahmadu Chindaya ya fitar.
Ya ce sun samu sanarwar nadin ne ta wata wasika da Ministan Lafiya Dokta Osagie Ehnire ya aike musu.
Sanarwar ta bayyana cewa, nadin zai fara aikin daga ranar 20 ga watan Agusta, 2022, kuma zai rike matsayin tsawon shekaru hudu.
Da yake mika takardar nadin, Ministan ya umarce shi da ya dage wajen daga darajar Asibitin da kuma inganta tattalin arziki, da tabbatar da ya bai wa marada kunya.
“Sashin lafiya wani muhimmin bangare ne ga tattalin arzikin kasa, ya kamata ka yi ƙoƙarin inganta shi”, in ji Ehanire.
Sanarwar ta ruwaito sabon Sabon Daraktan ya nuna jin dadinsa kan nadin, tare da tabbatar da cewa zai yi aiki tare da masu ruwa da tsaki wajen inganta asibitin.