Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da nadin sabbin Manayan Sakatarori hudu a ma’aikatun Gwamantin Tarayya.
Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Folasade Yemi-Esan ta sanar da haka, ta wata sanarwa da Darektar Yada Labarai a ofishinta, Olawunmi Ogunmosunle, ta fitar.
- Babu hannun gwamnati a kashe-kashe —Mailafia
- Hukumar DSS ta gayyaci Mahadi Shehu
- Farashin kayan abinci ya tashi —Ministar Kudi
Sabbin Manyan Sakatarorin su ne James Sule daga Jihar Kaduna da kuma Ismaila Abubakar daga Kebbi. Na ukun ita ce Ibiene Patricia Roberts daga Jihar Ribas sa kuma Aliyu Shinkafi Shehu daga Jihar Zamfara.
Sanarwar ta ce nan gaba za a sanar da ranar da za a rantsar da su da kuma ma’aikatun da za a tura su.